Dokar sirri ta Yaɗa bayanan kasuwa a Wurin-aiki

Farawa daga 10 Oktoba, 2023
JADAWALIN ABUBUWA
  1. Bayanin doka
  2. Bayanan da muke tattarawa
  3. Yadda muke sarrafa bayananka
  4. Bayanan da Mukan Raba
  5. Yadda za ka aiwatar da ‘yancinka
  6. Riiƙe bayananka
  7. Ayyukanmu na faɗin duniya
  8. Tushen dokokinmu don sarrafawa
  9. Sabuntawa zuwa ga Dokar Sirrantawa
  10. Wa ke da alhakin bayananka
  11. Tuntuɓe Mu

1. Bayanin Doka

Wannan dokar sirri (“Dokar Sirri”) tana bayani ne a kan aiwatar da datarmu haɗin guiwa da samar da kafarmu ta Shafin yanar gizo, da suka haɗa da Workplace.com (“Shafuka”) (a matsayin rarrabewa a tsakanin Ayyukan Workplace), sai kasuwancinmu da mayar da martani a kan ayyukanmu (a wuri ɗaya “Ayyuka”). A wannan Dokar Sirri, mukan fayyace bayanan da muka samo a kanka haɗin guiwa da shafukanmu da Shafinmu da Ayyukanmu. Daga nan mukan yi bayanin yadda mukan yi bibiya tare da raba wannan bayani da kuma yadda za ka iya aiwatar da ‘yancin da ka iya samu.
“Meta”, “mu”, “namu” ko “gare mu” na nufin ‘yancin Meta na ɗukar nauyin tattarawa da kuma amfani da bayanin mutum a ƙarƙashin Dokar Sirrin a amatsayin fitar da “Wanda ke da alhakin bayar da bayananka.
Ayyukan Workplace: Wannan Dokar sirri ba ta neman yin amfani da kayan Workplace da ke kan yanar gizo wadda muka samar ga abokan hulɗarmu, da kan bai wa masu amfana da mu su yi haɗin guiwa da raba bayanai a wurin aiki, dea suka haɗa da kayan Workplace, manhaja da kuma ayyukan da suka shafi yanar gizo (tare da “Ayyukan Workplace"). Amfaninka da Ayyukan Workplace ana jagorantarsa ne daga “Dokar Sirri ta Workplacenan.

2. Bayanan da muke tattarawa

Mukan tattara waɗannan bayanai a akanka.
Bayananka na tuntuɓa. Mukan tattara adireshinka na imel da kuma bayaninka na asali a matsayin sunanka, aiki, sunan wurin aiki da kuma lambar waya a lokacin, misali, a lokacin da ka nemi bayani haɗin guiwa da kayayyakinmu, da suka haɗa Workplace, sauke kayan aiki, shiga don kayayyakin kasuwanci, neman gwaji na kyauta ko halartar ɗya daga cikin tarukanmu ko hirarrakinmu. Idan ba za ka samar mana da wannan bayani ba. Ba ka da damar ƙirƙirar wani asusu don fara jaraba Workplace kyauta, ga misali. Idan ka kasance jami’in gudanar da asusun ma’aikatarku, mukan karɓi bayananka na tuntuɓa a lokacin da ka bayar da izinin karɓar bayanan kasuwancin da ke da alaƙa da hanyoyin sadarwa na zamani daga gare mu.
Bayanan da ka ba mu . A lokacin da ka tuntuɓe mu, za ka iya samar mana da wani bayanin. Yanayin bayanin ya dogara ne da dalilnka na tuntuɓar mu. Ga misali, idan kana da matsalar da take da alaƙa da yadda kake amfani da Shafukanmu, za ka iya samar mana da bayaninka ta hanyar la’akari da abin da zai taimaka a magance matsalarka, tare da ƙarin bayanin yadda za a tuntuɓe ka (misali, adireshin imel). Ga misali, za ka iya aika mana da imel tare da bayanin da ke da dangantaka da ƙwazon Shafin namu ko wasu batutuwan. Bugu da ƙari, idan ka tambaye mu a game da Ayyukan Workplace, misali, za ka iya shaida mana inda kake aiki ko wani bayanin da zai taimake mu wajen amsa ƙalubalenka.
Bincike da mayar martani. Kuma mun samu bayanai a kanka lokacin da ka zaɓi ka halarci ɗaya daga cikin bincike ko zaman mayar da martaninmu. Ga misali, muna aiki da wasu abokan hulɗa masu samar da ayyuka waɗanda suka yi bincike da kuma zaman mayar da martani a gare mu, kamar karɓr taron abokan hulɗa na Workplace waɗanda suka kasance a cikin zaman mayar da martani. Waɗannan kamfanoni sun samar mana da bayanan da suka samu a kanka a wani irin yanayi na ba-zata, da suka haɗa da shekarunka, jinsi, imel, bayanin kasuwancinka da kuma hanyoyin da kake amfana da kayayyakinnmu, sai kuma martanin da ka samar.
Shiga Da kuma Amfana da Bayanai . Muna tattara bayanai a kan aikinka a cikin Shafinmu, kamar dangantakar aiki, gwaji, da kuma tasirin bayani. Wannan ya ƙunshi bayani a kan aikinka (da ya ƙunshi yadda kake amfani da Shafinmu, da lokacin, adadi, da kuma tsawon lokacin ayyukanka), fayilolin shigarwa, da gwaji, cunkoso, yanar-gizo, sai shigar da ayyuka da rahotanni.
Na’ura Da Haɗa Bayani. Muna karɓar na’ura da haɗa ƙwaƙwaran bayanai a lokacin da kake shiga ko amfani da Shafinnmu. Wannan ya ƙunshi bayani kamar matsayin kayan zamani, tsarin tafiyar da bayani, matakin batiri, alamar ƙarfi, yanayi manhaja, bayanin burauza, wayar hnayar sadarwa, bayanin haɗa layuka (ya ƙunshi lambar waya, mai sarrafa waya ko ISP), harshe da yanayin lokaci, adireshin IP, bayanin sarrafa na’ura, sai masu fayyacewa (da suka haɗa da masu fayyacewa na daban ga Kayyaykin Kamfanin Meta masu alaƙa da wannan na’ura ko asusu).
Kukis. Shafukanmu suna amfani da kukis. Kuki wani ɗn ƙaramin abu ne na data da Shafinmu yakan aika ga mai amfani da burauza, wanda zai a iya adana shi a kan ma’ajiyar waje ta yadda za mu iya ganin na’uarar wanda ke amfana lokacin da suka dawo. Haka kuma, Mukan yi amfani da hanyoyin fasaha da sukan yi aiki iri ɗaya. Za ka iya koyon abubuwa da yawa a kan yadda muke amfani da kukis da irin wannnan fasaha a kan shafinmu na Workplace a cikin Dokar Kukis.
Bayanin Abokin Hulɗa na daban. A inda muke aiki da masu samar da ayyukan abokan hulɗa na daban don su taimake mu wajen sarrafa, samar, fahintar, maye gurbi, sai tallafa wa Shafukanmu ko Ayyukanmu, muna tattara bayanai daga gare su a kanka.
Kamfanonin Meta. Muna tattara bayanai daga ayyuka, salale, da rarraba fasaha da wasu kamfanonin Meta a wani yanayi na musamman. Kuma muna bibiyar bayanai a game da kai a dukkan kayyayakin Kamfanin Meta da kuma cikin na'urorinka a kan kowace dokar kaya kamar yadda aka bayar da lamuni a dokance.
Bayanan da aka tattara a lokacin da ka yi aiki da Ayyukan Workplace ya dogara ne a kan Dokar Sirri ta Workplace wanda ya jagoranci yadda aka bibiyi bayananka a lokacin da ka yi amfani da Ayyukan Workplace.

3. Yadda muke sarrafa bayananka

Mukan yi amfani da bayanan da muka (samu a kan zaɓin da ka yi da ɗabbaƙa doka) wajen sarrafa, samar da, inganta, fahintar, maye gurbi, sai tallafa wa Shafukanmu da Ayyukanmu.
Samar da, inganta da bunƙasa Sfafukanmu da Ayyukan mu.
Mukan tsettsefe bayananka don samar da, inganta da kuma bunƙasa Shafukanmu da Ayyukanmu. Wannan ya ƙunshi ƙyale ka wajen yin amfani na gaba ɗaya da duba shafukanmu, tuntuɓar mu don ƙarin bayani, shiga ƙarin kayayyakin aiki da yin rijistar gwaji na kyauta. Kuma za mu yi amfani da bayananka wajen fitar da ayyukan kasuwancinmu ta hanyar wannan Doka ta Sirri. Haka kuma mukan yi amfani da bayananka wajen samar da, inganta da faɗaɗa bincikenmu ko zaman martani da ka shiga.
Fahintar abin da Abokan hulɗa suke So da Buƙata.
Mukan yi la’akari da kuma tsettsefe bayananka tare da martani idan ka halarci zaman mayar da martani ko wani nazari (kamar a misali, inda ka gwada manufa da duba tsare-tsaren Workplace). Mukan yi wannan ne don fahintar abin da abokan hulɗa suke so da buƙata, ga misali, sanar da shin ko canji ko gabatar da sababbin tsare-tsare na Workplace ko wasu kayayyaki da ayyuka da kuma samun wasu bayanai. Bayanin da aka samu daga halartarka a zaman mayar da martani ko wani nazarin martani da za a tanatance da kuma amfani da sake-fayyace fom da yankin zance ko son-rai da akan yi amfani da shi a wajen martani ko rahoton sanya-idanu, rahoton ba zai danganta wannan da kai ba.
A yi sadarwa da kai.
Mukan yi amfani da bayanan da mu ke da su don aika maka bayanan kasuwancin sadarwa kuma mu sanar da kai game da Shafukanmu da Ayyukanmu, sannan mu sanar da kai a game da manufofi da sharuɗɗanmu a inda ya dace. Haka kuma mukan yi amfani da bayananka domin ba ka amsa a lokacin da ka tuntuɓe mu.
Samar da, na ƙashin kai, aunawa tare da inganta kasuwancinmu da tallatawa.
Za mu iya yin amfani da bayananka wajen manufar talla, da ta ƙunshi ta hanyar sadarwa ta farko da ta uku kuma don ƙirƙirar muryoyi masu kama da juna, asalin masu sauraro da awo a hanyar tallar sadarwa ta farko da ta uku
Yaɗa manufar kariya, mutunci da tsaro.
Mukan binciki na’urarka da kuma bayanan haɗawa don tatntancewa da binciko tsare-tsaren miyagun halaye.
Adanawa tare da yaɗa bayanai ga wasu da suka haɗa da jami’an tsaro da kuma mayar da amsa ga buƙatar doka.
Mukan sarrafa bayanai lokacin da muke biyayya da wajibcin doka da ya haɗa da, misali, domin shiga, adanawa ko bayyanar da wasu bayanai idan akwai ingantacciyar buƙatar doka daga hukumar sa ido, hukumomin tsaro ko wasu. Wannan ya ƙunshi mayar da amsa ga buƙatar doka a inda ba muka gaza bin doka sai dai kuma muna da kyakkyawan yaƙini cewa doka ce ta nemi hakan a wurare da dama na hukunci ko rarraba bayanai ta hanyar tilasta bin dokoki ko abokin hulɗar masana’antu don sauya ɓatanci ko ɗabi’ar ƙin bin doka. Ga misali, mun adana hotunan bayanin mai amfana a lokacin da aka nema daga mau kula da dokoki a inda ya dace da nufin bincike. Mun adana tare da rarraba bayanai a lokacin da muka buƙaci bayanin doka ko neman kare-kai a muhallin shari’a da sauran sa-in-sa. Wannan ya ƙunshi abubuwa kamar Saɓawa sharuɗɗanmu da manufofinmu. A wasu misalai, rashin samar mana da bayananka a lokacin da aka buƙata daga doka na iya kawo karya dokokin da aka shimfiɗa a gaer ka da kuma Meta.

4. Bayanan da Mukan Raba

Muna buƙatar abokan hulɗa da wasu daban su bi dokoki game da yadda za su iya amfani da rashin amfani da kuma bayyana bayanan nan da muke samarwa. Ga ƙarin bayani game da wanda muke yaɗa bayanai gare su:
Abokan hulɗa na daban da Masu samar da Ayyuaka: Muna aiki da abokan hulɗa da masu samar da aiki don taimaka mana wajen ɗukar nauyin Shafukanmu da Ayyukanmu. Ya danganta da yadda sukan tallafa ko aiki da mu, a lokacin da muka yaɗa bayanai tare da masu samar da ayyuka na daban a cikin wannan yanayi, mukan buƙace su don yin amfani da bayananka a madadinmu ta hanyar sharuɗɗanmu da dokokinmu. Muna aiki da abokan hulɗa da masu samar da ayyuka daban-daban, kawo sunayen waɗanda suka tallafa mana da kasuwanci, tsettsefwa, bincike, zaman martani, da kuma inganta kayayyaki da ayyuka.
Kamfanonin Meta: Mukan yaɗa bayanan da muke tattarawa, haɗin guiwa da Ayyukanmu ko ta Shafukanmu. Abubuwan more rayuwa, tsare-tsare da fasaha tare da sauran Kamfanonin Meta. Yaɗawa kan taimaka mana wajen bunƙasa kariya, tsaro da inganci; mayar da tayi da ma kaya; biyayya ga dokokin da aka kafa; bunƙasa da kuma samar da tsare-tsare da ma inganci; tare da fahintar yadda mutane sukan yi amfani da kuma cuɗanya kayan kamfanin Meta.
Doka da Biyayya: Za mu iya shiga, adanawa, amfani da kuma yaɗa bayananka (i) don bayar da amsa ga buƙatun doka, kamar binciko laifuffuka, umurnin kotu, umurnin samarwa ko sammace. Waɗannan buƙatu kan zo daga wasu daban kamar farar hula masu ƙara, jami’an tsaro da saura hukumomin gwamnati. Kuma za mu iya yaɗa bayananka da ma wasu hukumomi, da suka haɗa da kamfanonin Meta ko abokin hulɗa na daban, waɗanɗa sukan taimaka mana wajen binciko tare da ba mu amsar irin waɗancan bukatu, (ii) don bunƙasa kariya, tsaro da ingancin Kayayyakin Meta, masu amfana, ma’aikata, dukiya da kowa ma. Wannan ya ƙunshi dalilan binciken rashin cika yarjejeniya, karya dokar sharuɗɗanmu da dokokinmu ko keta doka ko ɓata, adireshi ko kariya daga zamba. Bayananka na ƙashin kai kuma za su iya samuwa a inda ya zama wajibi don kafawa, aiwatarwa, ko kariya ga ƙorafe-korafen doka sai kuma binciko ko kare zahiri ko asarar da ake zargi ko ɓatanci ga wasu ko dukiya.
Sayar da Kasuwanci: Idan muka sayar ko aika dukkan kasuwancinmu ko wani ɓangarensa zuwa ga wani, to za mu ba wa sabon mai mallaka bayananka a matsayin wani sashe na wannan kasuwanci, a bisa ga dokar da aka samar.

5. Yadda za ka aiwatar da ‘yancinka

Kana da ‘yanci dangane da bayananka na ƙashin kai, ya dogare ne a kan dokokin da aka sanya da kuma inda kake da zama. A inda aka sanya wasu daga cikin waɗannan dokoki, irin waɗannan haƙƙoƙi akan sanya su ne a cikin ƙananan laifuka ne kaɗai ko a wasu shari’o’i. Za ka iya aiwatar da ‘yancinka ta hanyar tuntuɓar muta nan.
  • ‘Yancin shiga/sanin - Kana da ‘yancin neman izinin shiga bayananka sannan a samar da shi a wani kwafi na wannan bayani da ya haɗa da ɓangarorin bayanaka na ƙashin kai da muka samu, amfani, da bayyanawa, sai bayani a kan aiki da data.
  • ‘Yancin Tabbabatarwa - Kana da ‘yancin neman tababbatar da bayanai na ƙashin kai da ba su cika ba a game da kai.
  • ‘Yancin gogewa/sharewa - Kana da ‘yancin, a wasu lokuta, ka nemi da mu goge bayananka na ƙashin kai, samar da hujjoji na gaskiya don yin hakan da kuma daidai da dokokin da aka shimfiɗa.
  • ‘Yancin tattala data - Kana da ‘yancin karɓa, a wani yanayi, bayananka a tsare, amfani da shi haka nan da tsarin na’urar-karatu sai sauya wannan bayani ga wani mai kulawa.
  • ‘Yancin ƙalubale/kwarmato (tallatawa) - Kana da ‘Yancin ƙalubalanta wajen sarrafawa don kasuwanci kai tsaye, cikakke kuma tabbataccen ƙuduri da kan haddasa dalilai a kowane lokaci . Idan muka yi amfani da bayananka don kasuwanci kai tsaye, za ka iya ƙalubalanta da kwarmata saƙonnin kasuwanci ta hanyar amfani da kafar da ba a tabbatar da ita ba a irin wanccan sadarwa.
  • ‘Yancin ƙalubalanta - Kana da damar ƙalubalanta da kange sarrafa bayananka. Za ka iya ƙalubalanta a kan sarrafa bayananka a yayin da muka dogara da ra’ayin na kan doka ko muka yi wani aiki a kan ra’ayin jama’a. Za mu yi la'aƙari da abubuwa da dama a yayin da muke ƙimanta ƙalubale, da suka haɗa da: Har sai lokacin da muka gano cewa muna da wasu halastattun dalilai na wannan sarrafawar, waɗanda muradunka ko cikakken haƙƙinka ba su rinjaye su ba ra’ayinka ba, ko kuma ana buƙatar sarrafawar ne domin wasu dalilai na shari’a, za a tabbatar da ƙin amincewarka, sannan za mu dakatar da sarrafa bayananka. Za ka iya yin amfani da kafar “ficewa” a tsarin sadarwar kasuwarmu don tsayar da mu amfani da bayananka domin tallatawa kai tsaye.
    • Tsammaninka Mai dalili
    • Alfanu da haɗurra gare ka, gare mu, sauran masu amfani ko wasu mutane na daban
    • Sauran abubuwan da ake da su domin cim ma manufa ɗaya marar haɗari da kuma wadda ba ta neman ƙoƙarin da bai dace ba
  • ‘Yancin warware izininka - A inda muke da ‘yancin bibiyar ka na wasu ayyuka, kana da ‘yancin warware waccan amincewa taka a kowane lokaci. Ka sani cewa rashin bin doka a cikin kowace yarjejeniya ba za ta shafi janyewar izininka ba.
  • ‘Yncin yin ƙorafi - Za ka iya shigar da ƙorafi ga ƙaramar hukumar da ke sanya ido. Meta Platforms Ireland Limited ya jagoranci duba hukumar na hukumar kariyar bayani ta Irish.
  • ‘Yanci na rashin nuna wariya: Ba za mu nuna bambanci gare ka saboda amfani da kowanne daga waɗannan dama ba.
Ka lura da cewa don kare bayananka da kuma mutuncin Kasuwancinmu, wataƙila mu buƙaci mu tantance shaidarka kafin mu sarrafa buƙatarka. A wasu lamurran, mai yiwuwa mu buƙaci tattara ƙarin bayanai domin tantance shaidar ka, kamar ID da gwamnati ta bayar a wasu shari’o’i. A ƙarƙashin wasu dokoki, za ka iya aiwatar da waɗannan ‘yancin kai da kanka ko kuma za ka iya wakilta wani wakili mai izini don ya miƙa waɗannan buƙatu a madadin ka.
Babbar Dokar Kaiyar Bayanai ta ƙasar Brazil
Wannan sashe ya shafi ayyukan sarrafa bayanai na ƙashin kai a ƙarƙashin dokar Brazil tare da ƙarfafa wannan Doka ta Sirri.
A ƙarƙashin Dokar Brazil ta Kariyar Bayanai ta Gabaɗaya (the “LGPD”), kana da haƙƙin shiga, yin gyara, matsarwa, gogewa, da kuma tabbatar da cewa mun sarrafa bayananka. A wasu lamurran, kana da damar ƙalubalanta da taƙaice sarrafa bayananka na ƙashin kai, ko kuma za ka iya janye amincewarka a yayin da muke sarrafa bayanan da ka ba mu bisa amincewar ka. Wannan Dokar Sirrantawa tana samar da bayani game da yadda muke yaɗa bayanai ga wasu daban. Don buƙatar ƙarin bayani game da tsare-tsarenmu a kan bayanai, danna nan.
Kuma kana da haƙƙin kai ƙorafi ga Hukumar Kare Bayanai ta Brazil ta hanyar tuntuɓar DPA kai tsaye.

6. Riiƙe bayananka

Za mu riƙe bayananka na ƙashin kai ne kaɗai idan ya kasance dole ne sai an fitar da dalila a wannan Doka ta Sirri. Meta za ta riƙe bayananka waɗanda mukan tattara a lokacin da ka halarci zaman mayar da martani ko nazarin mayar da martani a lokacin aikin da kuma wannan lokaci daga bisani kamar yadda aka buƙata wajen gudanar da bincike, bayar da amsa ga bibiya ta ƙwaƙƙwafi ko kuma dai tantance martani. Meta za ta riƙe da ma amfani da bayananka na ƙashin kai ta yadda har sai ya zama wajibi ya yi daidai da dokokin da suka wajaba (ga misali, idan muka buƙaci da mu riƙe bayannka na ƙashin kai don yin daidai da dokar da ta dace), wajen sasanta jayayya da kuma ƙarfafa sharuɗɗanmu. Da zaran waɗannan sharuɗɗa sun wuce sannan kuma ba da wani takamaiman dalili ba na riƙe wancan bayani na ƙashin kai, bayani na ƙashin kai da ya dace zai goge.

7. Ayyukanmu na faɗin duniya

Mu na yaɗa bayanan da muke tattarawa a faɗin duniya, duka a cikin ofisoshinmu da cibiyoyin bayanai, sannan a waje tare da masu yin aiki, masu samar da ayyuka da kuma wasu daban. Saboda Meta na duniya ne, tare da abokan hulɗa da ma’aikata a faɗin duniya, aikawa na da muhimmanci saboda dalilai daban-daban, da suka haɗa da:
  • Domin mu iya aiki da samar da ayyukan da aka faɗa a sharuɗɗan wannan Doka ta Sirri.
  • Don haka za mu iya sanywa, bincikawa da inganta kayyayakinmu haɗi da wannan Doka ta Sirri.
Ina ne ake aikawa da bayanai?
Za a aika ko watsa su ko watsa bayananka zuwa, ko a adana tare da sarrafa su a:
  • Wuraren da muke da kayan more rayuwa ko cibiyoyin bayanai, da suka haɗa da Amurka, Ireland, Denmark, Sweden, da sauransu
  • Ƙasashen da akan iya samun Workplace
  • Sauran Ƙasashe inda dillalai, masu samar da aiki da wasu daban suke da zama a wajen ƙasar da kake zaune, domin manufofi kamar yadda aka bayyana a wannan Doka ta Sirri.
Ta yaya muke kiyaye bayananka?
Mun dogara ne a kan wasu ingantattun dabaru domin yin sauyawar data na ƙasa da ƙasa.
Dabarun da muke amfani da su wajen tiransifar bayanai a duniya
Mun dogara ne a kan wasu ingantattun dabaru domin sauyawar bayanai na ƙasa da ƙasa. Alal misali, ga bayanin da muke tattarawa.
Wurin Tattalin Arziƙin Turai
  • Muna dogara ga shawarwari daga Hukumar Ƙasashen Turai inda suka yarda cewa wasu ƙasashe da iyakoki da ke wajen Yankin Tattalin Arziƙin Turai su tabbatar da wadataccen matakin kariya ga bayanan ƙashin kai. Waɗannan shawarwari ana kiran su da “wadatattun shawarwari”. Musamman ma, muna tura bayanan da muke tattarawa daga Yankin Tattalin Arziƙin Turai zuwa Argentina, Isira’ila, New Zealand, Switzerland, Birtaniya da kuma, inda shawarar ta dace, Canada bisa dogaro da wadatattun shawarwari da suka dace. Ƙara sanigame da ingantaciyar shawara ga kowace ƙasa, Meta Platforms, Inc. ta gamsu da halartar ta a EU-U.S. Tsarin Garkuwar Tsare Sirri. Mun dogara a kan EU-U.S. Tsarin Garkuwar Tsare Sirri, da kuma shawarar cancantar Hukumar Tarayyar Turai, don canja wurin bayanai don kayayyaki da ayyuka da aka ayyana a wannan shaida. Domin ƙarin bayani, yi bitar Meta Platforms, Inc.Tattaunawar Tsarin Garkuwar Tsare Sirri.
  • A wani yanayin, muna dogaro a kan Tsayayyun siɗirorin yarjejeniyarwadanda Hukumar Ƙasashen Turai ta amince da su (da makamantan tsayayyun siɗirorin yarjejeniya na Birtaniya, inda ya dace) ko akan wariya daga doka da aka samar ƙarƙashin dokar da ke aiki domin yin taransifar bayanai ga wata ƙasa ta daban.
  • Bugu da ƙari, daure ka karanta ƙarin matakai da muke ɗauka don canja wurin bayananka da kyau.
Idan kana da tambayoyi game da taransifar mu taƙasa da ƙasa da kuma tsayayyun siɗirorin yarjejeniya, za ka iya tuntuɓar mu.
Korea
Ƙara koyo game da sirrin haƙƙin mallaka da ke akwai gare ka, bayanai game da mutum na uku muka raba bayananka tare da wasu al’amuran ta sake duba Sanarwar tsarin Sirri ta Koriya.
ROW:
  • A wani yanayin, muna dogaro a kan Tsayayyun siɗirorin yarjejeniyar wadanda Hukumar Ƙasashen Turai ta amince da su (da makamantan tsayayyun siɗirorin yarjejeniya na Birtaniya, inda ya dace) ko akan wariya daga doka da aka samar ƙarƙashin dokar da ke aiki domin yin taransifar bayanai ga wata ƙasa ta daban.
  • Mun dogar ne a kan niyyar Hukumar Ƙasashen Turai, da sauran hukumomi, game da ko wasu ƙasashe suna da isassun matakan kariyar data .
  • Muna amfani da dabaru da suka dace a ƙarƙashin dokoki da suka shafi taransifar data zuwa Amurka da sauran ƙasashe.
Mukan kuma tabbatar da cewa, an samar da kiyayewar da ta dace a duk lokacin da muka aika da bayananka. Alal misali, mukan rufe bayananka a yayin da muke aika su daga ganin jama’a domin kare su daga faɗawa hannun da ba a bai wa damar shigar su ba.

8. Tushen Dokokinmu don Sarrafawa

A ƙarƙashin wata dokokin da aka samar ta kare bayanai, dole ne kamfanoni su kasance suna da madogara ta doka domin sarrafa bayanai na ƙashin kai. Idan muna magana a kan “sarrafa bayanai na ƙashin kai”, muna nufin hanyoyin da muke tattarawa, amfani da yaɗa bayananka, kamar yadda muka bayyana a sauran sassa na wannan Doka ta Sirri.
Mene ne madogararmu a dokance?
Dogaro ga tsarin dokoki daban-daban da kuma abin da ya bijiro maka, mun dogara ne a kan tushen doka daban don sarrafa bayananka ga manufar da aka bayyana a wannan Doka ta Sirri. Kuma za mu iya dogara a kan tushen doka daban-daban a yayin da muke sarrafa bayananka don manufofi daban-daban. A wasu shari’o’in, mun dogara ne a kan bayar da izini wajen shiga bayananka na ƙashin kai. A wasu shari’o’i, da suka haɗa da Yankin Turai, za mu dogare ne akan tushen dokkoin da ke ƙasa. Ga kowace madogara ta doka da ke ƙasa, muna bayyana dalilin da ya sa muke sarrafa bayananka.
Halastattun muradu
Mun dogara ne a kan halastattun muradunmu ko halastattun muradun abokan hulɗa na daban, inda ba muradunka ba su rinjaye su ba ko cikakkun haƙƙoƙi da ‘yanci ("halastattun muradu").
Dalili da kuma yadda muke sarrafa bayanankaHalastattun muradun da aka dogara a kaiKashe-kashen amfani da bayanai
Don samar da, inganta da bunƙasa Sfafukanmu da Ayyuka, mu:
Tace bayananka da kuma yadda za ka yi amfani da Shafinmu da kuma amfani da kasantuwa a kan Ayyuka..
Yana daga cikin buƙatarmu wajen fahintar ayyukan Shafinmu sai kulawa da kuma inganta Shafin namu.
Yana daga cikin bukatarmu wajen samar da Kasuwanci da ma Ayyukan Mayar da martani, don fahintar yadda kake amfani da waɗannan, sai kuma bunƙasawa da inganta su.
  • Bayananka na Tuntuɓa
  • Bayanan da Ka Ba Mu.
  • Shiga da kuma Amfana da Bayanai
  • Na’ura Da Haɗa Bayanai.
  • Bayanin Abokin Hulɗa na daban
  • Kukis
Don fahintar abin da masu yin amfani suke bukata da so:
Samar da Ayyukanmu, da suka haɗa da tsettsefe bayananka da amsarka idan ka haklarci zaman mbayar da amsa da wani nazari a kan mayar da martani, ga misali ka gwada sababbin bayanai.
Bayanan da muka samu daga haklartarka a zaman mayar da martani da sauran nazarin bayar da amsa za a ƙwanƙwance shi da kuma yin amfani da shi a wajen sake tantance fom kuma idan an yi amfani da yankin bayani ko son rai a wajen martani ko rahoton sa-idanu, to rahotan ba zai ja hankalinka da wannan ba.
Yana cikin abin sha’awarmu a cikin sha’awar abokan hulɗa suke so da buƙata, don sanin abin da abokan hulɗarmu suke so da buƙata sai kuma amfani da wannan wajen sanar da shin ko canji ko gabatar da sababbin tsare-tsare na Workplace ko wasu kayayyaki da ayyuka da kuma samun wasu bayanai.
  • Bayananka na Tuntuɓa
  • Bayanan da Ka Ba Mu.
  • Shiga da kuma Amfana da Bayanai
  • Na’ura Da Haɗa Bayanai.
  • Bayanin Abokin Hulɗa na daban
  • Kukis
Don tattaunawa da kai da kuma aika maka da kasuwancin sadarwa (a inda ba su yi daidai da bayar da izini ba).
idan ka yi rijistar karɓar kasuwancin sadarwa ta imel kamar muhimman bayanan da aka buga, za ka iya fita a kowane lokaci ta hanyar danna kafar “unsubscribe” a kowane lokaci da ya haɗa da ƙasan kowane imel.
Muna tattaunawa da kai a game da Ayyukanmu da dokokinmu ko sharuɗɗanmu waɗanda suka dace.
Kuma muna ba da amsa a gare ka a lokacin da ka tuntuɓe mu.
Yana daga cikin buƙatarmu wajen aika maka kasuwancin sadarwa kai tsaye don tallata kayayyakinmu da kuma samar maka da bayanai a kan sabo ko sabunta kayayyakin da ake buƙata.
Yana daga cikin buƙatarmu da kuma buƙatarka a kan Ayyukanmu.
Yana daga cikin buƙatarmu da bukatarka wajen yin amfani da bayananka don ba ka amsa a lokacin da ka tuntuɓe mu.
  • Bayananka na Tuntuɓa
  • Bayanan da Ka Ba Mu.
Don samar da, mallaka, aunawa da kuma inganta kasuwancinmu da tallatawa, mu:
Yi amfani da bayananka wajen manufar talla, da ta ƙunshi ta hanyar sadarwa ta farko da ta uku kuma don ƙirƙirar muryoyi masu kama da juna, asalin masu sauraro da awo a hanyar tallar sadarwa ta farko da ta uku
Yana daga cikin buƙatarmu ta ɗaukar nauyin kasuwanci da kuma tallata ayyuka.
  • Bayananka na Tuntuɓa
  • Bayanan da Ka Ba Mu.
  • Shiga Da kuma Amfana Da Bayanai.
  • Na’ura Da Haɗa Bayanai
  • Kukis
Don bunƙasa kariya, inganci da kuma tsaro, mu:
Binciki na’urarka da kuma bayanan haɗawa don tatntancewa da binciko tsare-tsaren miyagun halaye.
Yana daga cikin buƙatarmu da kuma buƙatar masu amfani da Shafukanmu da masu shiga kasuwancinmu da Ayyukan Bayar da Amsa don ayyukan da ke da kariya da kuma yaƙar sifam, zagi, ko ayyaukan zamba da bunƙasa kariya da ma tsaro a kan Shafukanmu da Ayyukanmu.
  • Na’ura Da Haɗa Bayanai
  • Shiga Da kuma Amfana Da Bayanai.
  • Kukis
Mun adana da kuma yaɗa bayanai tare da sauran da suka haɗa da tilasta bin doka sai kuma bayar da amsa ga buƙatun doka.
Wannan ya ƙunshi mayar da amsa ga buƙatar doka a inda ba muka gaza bin doka sai dai kuma muna da kyakkyawan yaƙini cewa doka ce ta nemi hakan a wurare da dama na hukunci ko rarraba bayanai ta hanyar tilasta bin dokoki ko abokin hulɗar masana’antu don sauya ɓatanci ko ɗabi’ar ƙin bin doka. Ga misali, mun adana hotunan bayanin mai amfana a lokacin da aka nema daga mau kula da dokoki a inda ya dace da nufin bincike.
Yana daga cikin buƙatunmu da ma buƙatun abokan hulɗarmu wajen karewa da kuma magance zamba, amfani da Shafi a kan rashin amincewa, ko wani haramtacce ko ɓataccen aiki.
Yana daga cikin bukatarmu wajen kare kanmu (da ya haɗa da ‘yancinmu, ayyuka, dukiyoyi ko kayayyaki), abokan hulɗarmu ko wasu, da suka haɗa da wani ɓangaren bincike ko bayanin ƙayyadewa; ko kare mutuwa ko ɓataccen jiki mai yawa.
Tilasta bin dokoki, gwamnati, hukumomi kuma abokan hulɗar masana’anta suna da halastacciyar bukata a wajen bincike da kuma musanya zagi ko halayyar da ba ta kan doka.
  • Bayananka na Tuntuɓa
  • Bayanan da Ka Ba Mu.
  • Na’ura Da Haɗa Bayanai
  • Shiga da kuma Amfana da Bayanai
  • Bayanin Abokin Hulɗa na daban
  • Kukis
Mun adana tare da rarraba bayanai a lokacin da muka buƙaci bayanin doka ko neman kare-kai a muhallin shari’a da sauran sa-in-sa. Wannan ya ƙunshi abubuwa kamar Saɓa wa sharuɗɗanmu da manufofinmu, a inda ya dace.
Yana daga cikin buƙatarmu da kuma buƙatar abokan hulɗarmu wajen bayar da amsa ga ƙorafe-ƙorafe, kare da kuma magance zamba, yin amfani da Shafukanmu ba tare da izini ba, Ayyuka, karya sharuɗɗanmu da dokokinmu a inda aka suka dace, ko wani ɓatacce ko aikin da ya saɓa wa doka.
Yana daga cikin buƙatarmu wajen neman bayanin dokoki da kuma kare kanmu (da ya haɗa da haƙƙoƙinmu, ayyuka, dukiyoyi ko kayayyaki), abokan hulɗa ko wasu, da suka haɗa da ɓangaren bincike ko tuntuɓar ƙayyadewa da zama gaban shari’a ko wani saɓani.
  • Bayananka na Tuntuɓa
  • Bayanan da Ka Ba Mu.
  • Na’ura Da Haɗa Bayanai
  • Shiga da kuma Amfana da Bayanai
  • Bayanin Abokin Hulɗa na daban
  • Kukis
Izininka
Mukan bi bayanai don manufofin da aka bayyana a ƙasa a lokacin da ka ba mu izini . An bayyana irin nau’in bayanin da ake amfani da ita da yadda ake aiwatar da ita a ƙasa.
Dalili Da Kuma Yadda Muke Sarrafa BayanankaKashe-kashen amfani da bayanai
Don aikawa da kasuwancin sadarwa (a inda ya kasance da izininka), A lokacin da muka bibiyi bayananka dangane da amincewarka, kana da ‘yancin ka janye izinin naka a kowane lokaci ba tare da ya shafi rashin bin doka ba wajen bibiya a kan wancan izini, kafin a janye izinin ta hanyar tuntuɓar mu da amfani da bayanan tuntuɓa da aka fitar a ƙasa.
Za ka iya ƙin shiga daga imel ɗin kasuwancin sadarwa a kowane lokaci ta hanyar danna kafar “unsubscribe” da ya haɗa da ƙarshen ko wane imel.
  • Bayananka na Tuntuɓa
Yin Biyayya Ga Dokokin da suka Wajaba
Mukan sarrafa bayanai ldon yin biyayya ga wajibcin doka da ya haɗa da, misali, domin shiga, adanawa ko bayyanar da wasu bayanai idan akwai ingantacciyar buƙatar doka.
Dalili Da Kuma Yadda Muke Sarrafa BayanankaKashe-kashen amfani da bayanai
Don sarrafa bayanai a lokacin da muke biyayya da wajibcin doka da ya haɗa da, misali, domin shiga, adanawa ko bayyanar da wasu bayanai idan akwai ingantacciyar buƙatar doka daga hukumar sa ido, hukumomin tsaro ko wasu. Ga misali, a binciko izini ko odar kaya daga tilasta bin dokokin Irish don samar da bayanai masu dangantaka da bincike, kamar adireshinka na IP.
  • Bayananka na Tuntuɓa
  • Bayanan da Ka Ba Mu.
  • Na’ura Da Haɗa Bayanai
  • Shiga da kuma Amfana da Bayanai
  • Bayanin Abokin Hulɗa na daban
  • Kukis
Kariyar Muhimman Buƙatunka Ko Kuma Waɗansu Na Wani
Muna bibiyar bayanai a lokacin da buƙatun wani masu muhimmanci suke neman kariya.
Dalili Da Kuma Yadda Muke Sarrafa BayanankaKashe-kashen amfani da bayanai
Muna yaɗa bayanai, da ya haɗa da jami’an tsaro, da sauransu, a yanayin da muhimman muradun wani ke buƙatar kariya, kamar a al’amuran ɗaukin gaggawa. Waɗannan muhimman ra’ayoyi sun haɗa da kare rayuwarka ko rayuwar wani, lafiyar jiki ko ta hankali, walwala ko mutunci ko na wasu
  • Bayananka na Tuntuɓa
  • Bayanan da Ka Ba Mu.
  • Na’ura Da Haɗa Bayanai
  • Shiga da kuma Amfana da Bayanai
  • Bayanin Abokin Hulɗa na daban
  • Kukis

9. Sabuntawa zuwa ga Dokar Sirrantawa

Za mu iya gyara ko sabunta Dokarmu ta Sirri daga lokaci zuwa lokaci. Za mu buga sabuwar Dokar Sirri, sabunta “Tsakiyar Karshe” kwanan wata daga sama da kuma duk wasu sauran matakai da aka sanya. Sake duba Doakarmu ta Sirri daga lokaci zuwa lokaci.

10. Wa ke da alhakin bayananka

Za mu iya gyara ko sabunta Dokarmu ta Sirri daga lokaci zuwa lokaci. Za mu buga sabuwar Dokar Sirri, sabunta “Tsakiyar Karshe” kwanan wata daga sama da kuma duk wasu sauran matakai da aka sanya. Sake duba Doakarmu ta Sirri daga lokaci zuwa lokaci.
Idan kana zaune a ƙasa ko tarayya a “Yankin Turai” (wanda ya ƙunshi ƙasashe a cikin Ƙungiyar Ƙasashen Turai da sauransu: Andorra, Austiyria, Azores, Belgium, Bulgaria, Canary Islands, Channel Islands, Croatia, Czech Republic, Denmark, Estonia, Finland, France, French Guiana, Germany, Gibraltar, Greece, Guadeloupe, Hungary, Iceland, Ireland, Isle of Man, Italy, Latvia, Liechtenstein, Lithuania, Luxembourg, Madeira, Malta, Martinique, Mayotte, Monaco, Netherlands, Norway, Poland, Portugal, Republic of Cyprus, Réunion, Romania, San Marino, Saint-Martin, Slovakia, Slovenia, Spain, Sweden, Switzerland, United Kingdom, United Kingdom sovereign mazauna Cyprus (Akrotiri da Dhekelia), da Birnin Vatican) ko kana zaune a wajen Amurka ko Canada mai kula da bayani ya dogara ne a kan bayananka na Meta Platforms Ireland Limited.
Idan kana zaune a Amurka ko Kanada Meta Platforms Inc shi ke da alhakin sarrafa bayananka.

11. Tuntuɓe Mu

Idan kana da tambayoyi a game da wannan Doka ta Sirri, ko samun tambayoyi, ƙorafe-ƙorafe ko buƙatu a game da bayananka da dokokinmu na sirri da ma aiwatar da su, za ka iya tuntuɓar mu. Za ka iya tuntuɓar mu yanar gizo, ta imel a workplaceprivacy@fb.com, ko ta mel at:
US & Canada:
Meta Platforms, Inc.
ATTN: Aikatar da Sirrintawa
1601 Titin Willow
menlo Park, CA 94025
Sauran Duniya (ys ƙunshi Yankin Turai):
Meta Platforms Ireland Limited
Merrion Road
Dublin 4
D04 X2K5
Ireland
Za a iya tuntuɓar Jami’in Kare Bayanai na Meta Platforms Ireland Limited a nan.