Sharuɗɗan Aiki na Wurin Aiki
KA BAYAR DA GARANTI TARE DA GABATAR DA CEWA KANA SHIGA WAƊANNAN SHARUƊƊAN KAN INTANET NA WURIN AIKI (“YARJEJENIYA”) A MADADIN KAMFANI KO WANI ABIN DA DOKA TA KAFA, DA CEWA KANA DA CIKAKKEN IKO NA ƘULLA WANNAN ABIN DOKA GA WANNAN YARJEJENIYA. NUNIN DA ZA SU BIYO BAYA GA “KAI”, “NAKA” KO “ABOKIN CINIKI” YANA NUFIN WANNAN ABIN
Idan kana da babban murin kasuwancinka a Amurka ko Canada, wannan yarjejeniya ce tsakanin ka da Meta Platforms, Inc. Ko kuma, wannan yarjejeniya ce tsakaninka da Meta Platforms Ireland Ltd. Mahanga da “Meta”, “mu”, “mu”, ko “namu” yana nufin ko dai Meta Platforms, Inc. ko kuma Meta Platforms Ireland Ltd., kamar yadda ya dace.
Waɗannan sharuɗɗan za su yi aiki kan amfanin da za ka yi da Wurin-aiki. Ka amince cewa sigogi da tsarin aiki na Wurin-aiki za su iya bambanta, kuma za su iya canjawa a tsawon lokaci.
An ba da ma’anar wasu sharuɗɗan masu babban baƙi a cikin Sashe na 12 (Ma’anoni) kuma an ba da ma’anar sauran a rubuce a cikin yarjejeniyar.
- Amfani da Wurin-aiki
- Haƙƙoƙinka na Amfani. A lokacin Wa’adin, kana da haƙƙin da ba keɓaɓɓe ba, wanda ba a musayar sa, wanda ba a raba lasisinsa don shiga da kuma amfani da Workplace a bisa wannan yarjejeniya. Amfani da Workplace ya taƙaita ga Masu Amfani (da suka haɗa da, inda ya dace, waɗanda suke ƙarƙashinka) waɗanda ka ke ba ds damar asusu don su, kuma kai ke da alhakin dukkan Masu Amfani da yadda suke biyayya da wannan Yarjejeniya da kuma damar su ta shiga, da amfani da, Workplace. Don fayyacewa, ana samar da Workplace a matsayin aiki gareka, ba ga ɗaiɗaikun Masu Amfani ba.
- Asusu. Dole bayanan rijista da na asusun gudanarwa su kasance sahihai, cikakku sannan waɗanda ake sabuntawa. Asusun Mai Amfani na ɗaiɗaikun Masu Amfani ne kuma ba za a iya yaɗawa ko tura su ba. Dole ka kiyaye sirrin bayanan shiga ciki kuma ka yarda za ka sanar da Meta nan take idan ka gano duk wani amfani da asusunka ko bayanan shiga ciki ba da izini ba.
- Taƙaicewa. Ba za ka (kuma ba za ka ba da izini ga wani daban ba don): (a) yin amfni da Wurin-aiki a madadin duk wani na daban ko yin haya, doguwar haya, samar da damar shiga ko raba lasisin Workplace ga duk wani na daban, ban da Masu Amfani kamar yadda aka ba da izini a cikin nan; (b) juya ƙirar fasaha, warware, wargaje, ko kuma neman samun lambar shiga Workplace, sai dai zuwa maƙurar da dokar da ke aiki ta ba da dma (kuma nan sai dai in an fara aika sanarwa ga Meta); (c) kwafa, gyarawa ko ƙirƙirar ayyukan da aka samo daga Workplace; (d) cire, gyarawa ko ɓoye duk wata mallaka ko wasu sanarwa da ke cikin Wurin-aiki; ko (e) yaɗa bayanan aiki dangane da aikin Workplace a bainar jama’a.
- Kafawa. Yayin kafa al’amarin Workplace ɗinka, za ka naɗa mai amfani ɗaya ko fiye da haka a matsayin mai gudanar da tsari na al’ummar Workplace ɗinka wanda ke da alhakin kula da al’amarin Workplace ɗinka. Dole ka tabbatar kana da aƙalla mai gudanar da tsari ɗaya da ke aiki don al’amarin Workplace ɗinka a dukkan lokuta.
- API na Wurin-aiki. A yayin Zangon, Meta zai iya samar maka da API na Workplacei ɗaya ko fiye da haka, domin ka samar da kuma amfani da ayyuka da manhajoji da suke ƙarfafa amfanin da ka ke da Workplace. Duk wani amfani da API na Workplace da kai, Masu Amfaninka, ko duk wani na daban a madadinka zai kasance ƙarƙashin tanade-tanade na Sharuɗɗan Dandamalin Workplace da suke aiki, da yanzu ake samu a workplace.com/legal/WorkplacePlatformPolicy, kamar yadda Meta zai riƙa gyarawa daga lokaci zuwa lokaci.
- Tallafi. Za mu samar da tallafin Workplace gare ka ta hanyar madannin tallafin kai tsaye a cikin bigiren gudanarwa na Workplace (“Hanyar Tallafin Kai tsaye”). Za ka iya miƙa buƙatar samun tallafi domin warware wata tambaya, ko kai rahoton wata matsala, dangane da Workplace, ta hanyar fitar da tikiti ta cikin Hanyar Tallafin Kai tsaye (“Tikitin Tallafi”). Za mu samar da amsar farko ga kowane Tikitin Tallafi cikin sa’o’i 24 daga lokacin da ka sami tabbatarwar imel cewa an fitar da Tikitin Tallafi ɗinka ta cikin Hanyar Tallafin Kai tsaye.
- Bayanai da Wajibcinka
- Bayananka. Ƙarƙashin wannan Yarjejeniya:
- za ka riƙe dukkan haƙƙi, mallaka da kuma muradi (da ya haɗa da haƙƙoƙin fasahar ilimi) a ciki da kuma ga Bayananka;
- a yayin Zangon, ka bai wa Meta damar da keɓaɓɓiya ba, ta duniya baki ɗaya, marar kamasho, mai cikakken biya don amfani da Bayananka kaɗai domin samar da Workplace (da madangancin tallafi) gare ka, bisa wannan Yarjejeniya; da kuma
- ka amince cewa Meta shine mai sarrafa bayanai da kuma cewa kai ne mai kula da bayanai na Bayananka, sannan ta hanyar shiga cikin wannan Yarjejeniya ka ba da umarni ga Meta ya sarrafa Bayananka a madadinka, domin manufofin da aka fasalta a cikin wannan Yarjejeniya kaɗai da kuma bisa tanadin wannan Yarjejeniya (da ya haɗa da Ƙarin Dokar Sarrafa Bayanai).
- Wajibcinka. Ka yarda (a) cewa kai ke da alhakin sahihanci da abin da ke cikin Bayananka; (b) don samun dukkan haƙƙoƙi da amincewar da suka wajaba waɗanda Dokoki suka buƙata daga Masu Amfaninka da kuma duk wani na daban da ya dace domin ba da damar tattarawa da amfani da Bayananka kamar yadda aka ƙudurta a cikin Yarjejeniyar; da kuma (c) cewa amfanin da ka ke da Workplace, da ya haɗa da Bayananka da amfaninsu a ƙarƙashin nan, ba zai saɓa duk wasu Dokoki ko haƙƙoƙin wani na daban ba, da ya haɗa da haƙƙoƙin fasahar ilimi, kadara, sirri ko na watsa bayanai ba. Idan duk wasu daga cikin Bayananka da aka miƙa ko aka yi amfani da su bisa saɓa wannan Sashe na 2, ka yarda ka cire shi nan take daga Workplace. Kai ne kaɗai ke da alhakin zartas da duk wata shawara don yaɗa Bayananka a tsakanin Masu Amfani ko ga duk wasu na daban, kuma Meta ba shi da alhakin yin amfani, shiga, jirkitawa, rarrabawa ko goge Bayananka daga wadanda kai ko Masu Amfaninka suka samar da su.
- Bayanan da aka Haramta. Ka yarda ba za ka miƙa ga Workplace duk wani bayani ko bayanai da suke da tsaro da/ko taƙaicewa akan rarrabawa ƙarƙashin dokokin da ke aiki da/ko hukumomin sa ido (“Bayanin da aka Haramta”). Dangane da bayanan lafiya, ka yarda cewa Meta ba Takwaran Kasuwanci ba ne ko ƙaramin ɗan kwangila (kamar yadda aka fasalta waɗancan sunaye a cikin Dokar Inshorar Lafiya da Bin Ƙa’ida (“HIPAA”)) da kuma cewa Workplace ba ya aiki da HIPAA. Meta ba zai ɗauki wani alhaki ƙarƙashin wannan Yarjejeniya don Bayanin Da Aka Haramta ba, ba tare da la’akari da duk wani abu sabanin haka ba.
- Diyyar ramako. Za ka kare, biya diyyar ramako kuma ba za ka cutar da Meta (da Waɗanda ke Ƙarƙashina da kuma daraktocinsu, jami’ai, dillalai, wakilai, da wakilai ba) daga da kuma akan duk wasu iƙrari (daga wasu na daban da/ko Masu Amfani), farashi, illa, nauyace-nauyace da kashe kuɗaɗe (da ya haɗa da kuɗaɗen lauyoyi madaidaita) da ke tasowa aga ko dangane da saɓawarka ko zargin saɓawa wannan Sashe na 2 ko kuma mai alaƙa da Bayananka, Manufofinka ko amfanin da ka ke da Workplace a saɓawa wannan Yarjejeniya. Meta zai iya shiga cikin kariya da biyan duk irin wannan iƙrari tare da lauyansa kuma da kuɗin aljihunsa. Ba za ka biya duk wani iƙrari ba tare da rubutacciyar amincewar Meta da aka samu da farko ba idan biyan yana buƙatar Meta ya ɗauki wani mataki, ya ƙi ɗaukar wani mataki, ko ya amince da duk wani alhaki.
- Ajiyar Ko-ta-kwana da Goge Bayanai. Meta baya samar da aikin adanawa, kuma kai kaɗai ke da alhakin ƙirƙirar ajiyar ko-ta-kwana na Bayananka. Za ka iya goge Bayananka da suka ƙunshi bayanin Mai Amfani a kowane lokaci sharuɗɗan ta hanyar aikin mai gudanar da tsarin Workplace.
- Jimillar Adadin Bayanai. Ƙarƙashin wannan Yarjejeniya, za kuma mu iya samar da jimillar adadin ƙididdiga bayanan nazari da aka samo daga amfanin ka na Workplace (“Jimillar Adadin Bayanai”), amma waɗannan Jimillar Adadin Bayanai ba za su haɗa da Bayananka ko duk wasu bayanin ƙashin kai ba.
- Bayananka. Ƙarƙashin wannan Yarjejeniya:
- Tsaron Bayanai
- Tsaron Bayananka. Za mu yi amfani da matakan da suka dace na aiki, na hukuma da kuma tsaro da aka tsara don kare Bayananka da ke hannunmu daga damar shiga, jirkitawa, bayyanarwa ko lalatawa marar izini, kamar yadda aka ƙara fasaltawa a cikin Ƙarin Tsaron Bayanai.
- Bayyanawar Doka da Buƙatun Wasu na Daban. Gaba ɗaya kai ne ke da alhakin ba da amsa ga buƙatar wasu na daban da ya shafi Bayananka, kamar daga masu kula Masu Amfanii, ko hukumar ɗabbaƙa doka (“Buƙatar Wasu na Daban”), amma ka fahimci cewa, a bayar da amsa ga Buƙatar Wani na Daban, Meta na iya bayyanar da Bayananka don yin biyayya ga buƙatunsu na doka. A irin waɗannan lamura, za mu, zuwa maƙurar da doka ta ba da dama da kuma bisa sharuɗɗan Buƙatun Wasu na Daban, yi amfani da ƙoƙarin da ya dace mu (a) sanar da kai mun karɓi Buƙatar Wani na Daban sannan mu nemi wani na daban ya tuntuɓe ka da kuma (b) yin aiki da buƙatunka da suka dace dangane da ƙoƙarinka na jayayya da Buƙatar Wani na Daban da nauyin zai hau kanka. Da farko za ka nemi samun bayanin da aka buƙata don ba da amsa ga Buƙatar Wani na Daban akan kanka, kuma za ka tuntuɓe mu ne kawai idan ba za ka iya samun wannan bayani yadda ya dace ba.
- Biyan Kuɗi
- Kuɗin biya. Ka yrda za ka biya Meta tsayayyen farashi na Workplace (da yanzu ake samu a nan: https://www.workplace.com/pricing) don amfanin da ka ke da Workplace, bisa ga duk wani wa’adin lokaci na gwajin kyauta kamar yadda aka fasalta a Sashe na 4.f (Gwaji Kyauta), sai dai kuma idan an yarda a rubutaccen daftari da aka sa-hannu. Za a biya dukkan kuɗaɗen biya ƙarƙashin wannan Yarjejeniya da Dalar Amurka, sai dai kuma idan an fayyace a cikin-kaya, ko kuma sai dai idan an yarda a rubutaccen daftari da aka sa-hannu. Za a biya dukkan kuɗaɗen biya gaba ɗaya a bisa hanyar biyan kuɗinka ƙarƙashin Sashe na 4.b. Duk wasu biyan kuɗi a makare za a cire cajin aiki daidai da kashi 1.5% a wata na adadin da za a biya ko adadin da doka ta ba da dama, duk wanda yake mafi ƙaranci.
- Hanyar Biyan Kuɗi. Yayin da ka shiga cikin wannan Yarjejeniya ka yarda za ka biya kuɗaɗen biya ƙarƙashin ɗaya daga nau’ika biyu na biyan kuɗi: (i) abokin ciniki na katin biyan kuɗi (ko dai biya kai tsaye ko ta hanyar wani dandamalin biyan kuɗi na daban), ko (ii) abokin ciniki da aka wa takardar neman biya, kamar yadda aka tabbatar a ganin dacewar Meta. Abokan ciniki na katin biyan kuɗi za su iya (a hukuncin Meta) zama abokan ciniki da aka wa takardar neman biya (da juyin haka) a bisa abubuwa kamar yawan Masu Amfani da kuma cancantar samun bashi, sai kuma Meta ya riƙe damar sake rarrabe ka a matsayin abokin ciniki na katin biyan kuɗi ko kuma abokin ciniki da aka wa takardar neman biya a kowane lokaci.
- Abokan Ciniki na Katin Biyan Kuɗi. Abokan ciniki na katin biyan kuɗi za a caji katin biyan kuɗin da aka ware musu don amfani na Workplace.
- Abokan Ciniki da Aka wa Takardar Neman Biya. Meta zai isar kafar samun bashi ga abokan ciniki da aka wa takardar neman biya sannan za a ba su takardun neman biya a tsarin wata-wata, sai dai kuma idan an yarda a rbutaccen daftari da aka sa-hannu. Idan aka rarrabe ka a matsayin abokin ciniki da aka wa takardar neman biya, za ka biya dukkan kuɗaɗe biya ƙarƙashin wannan Yarjejeniya, gaba ɗaya kuma tabbatattun kuɗaɗe daga gare mu, cikin kwanaki 30 daga ranar takardar neman biya.
- Ka yarda mu sami rahoton bashi na kasuwancinka daga hukumar samar da basussuka yayin amincewa da wannan Yarjejeniya, ko wani lokaci bayan nan.
- Haraji. An bayyana dukkan kuɗaɗe a keɓe daga duk wasu harajin da ke aiki, kuma ana buƙatar ka biya kuma ka ɗauki nauyin duk wani ciniki, amfani, GST, harajin VAT, harajin da ake cirewa daga tushe ko harajin fito, na gida ko na waje, dangane da hada-hada ƙarƙashin wannan Yarjejeniya, waɗanda ba haraji ba bisa ga kuɗaɗen shiga na Meta. Za ka biya dukkan adadin kuɗin da za a biya ƙarƙashin wannan Yarjejeniya gaba ɗaya ba tare da wata ramuwa biya, ƙaryata iƙrari, cirewa ko riƙe kuɗi. A yanayin da duk wani biyan kuɗi da ka yi ƙarƙashin wannan Yarjejeniya zai iya kasancewa ana cirewa ko riƙe kuɗi, za ka ɗauki alhakin yin biyan kuɗin da ya dace ga hukumomin haraji da suka dace da kuma alhakin biyan kuɗi don kuɗin-ruwa, hukunci, tara, ko makamantan nauyace-nauyace da kan faru daga kasawarka wajen tura waɗannan haraji ga sahihiyar hukuma ko ma’aikatar gwamnati a kan lokaci. Ka amince kuma ka yarda cewa kana amfani da Workplace a adireshin bil da aka jera a wannan yarjejeniyar ko kuma kamar yadda aka samar mana a rubuce sannan kuma idan wannan adreshin a Amurika yake, za mu caje ka harajin sayarwa ko na amfani dangane da wurin adireshin bil ɗinka. Idan Hukumar Haraji ta Amurika ta tabbatar cewa yakamata a ce Meta ya tattara haraji daga wajenka, kuma ka biya wannan haraji kai tsaye zuwa ga jiha, ka amince ka samar mana da shaidar cewa an biya wannan haraji (har a gamsar da wannan Hukuma ta Haraji) cikin kwanaki 30 daga lokacin da Meta ya rubuto buƙatar hakan. Ka yarda ka wanke mu daga duk wani biyan kuɗi da bai kai ba ko ƙin biyan kuɗin kowane haraji da hukunci da kuɗin ruwa.
- Dakatarwa. Ba tare da shafar sauran haƙƙoƙinmu a ƙarƙashin wannan Yarjejeniya ba, idan ba ka biya wani kuɗi ba zuwa ranar biyan kuɗin, to za mu iya dakatar duka ko wani ɓangare na ayyukan Workplace (haɗi da damar amfani da ayyukan da aka biya) har sai an kammala biyan kuɗin.
- Damar Amfani Da Workplace Har Abada Kyauta. Duk da cewa akwai Sashe na 4.a, idan ka nemi damar yin amfani kyauta a ƙarƙashin shirin Workplace Har Abada kuma Meta ya ga cewa ka cancanta bisa dokokin Meta (wanda a yanzu za a iya samun su a https://work.workplace.com/help/work/142977843114744), to za mu samar maka da Workplace ba tare da caji ba bisa tsarin wannan dokoki bisa tsarin ci gaba. Idan a sakamakon wani sauyi ga dokokinmu, ya zamana ba ka cancanci damar shiga kyauta ba, to Meta zai sanar da kai hakan wata uku (3) kafin nan sannan bayan wata ukun Sashe na 4.a zai yi aiki a kanka.
- Gwaji Na Kyauta Bisa raɗin kanta Meta yana ba ka damar gwajin Workplace a kyauta zuwa wani taƙaitaccen lokaci, lokacin da za a yanke shi bisa raɗin Meta a kuma sanar da kai ta hanyar fanel ɗin mai gudanarwa na Workplace ga misali. A ƙarshen wannan gwaji na kyauta Sashe na 4.a (kuɗi) zai yi aiki.
- Sirrantawa
- Wajibci Kowane ɓangare ya yarda cewa dukkanin bayanan kasuwanci da na fasaha da na kuɗi da ya samu (a matsayin “ɓangare mai karɓa”) daga ɓangaren da ya bayyana da ya danganci Yarjejeniya (“ɓangaren Mai Bayyanawa”) ya haɗar da sirrantawa ɓangaren Mai Bayyanawa (“Bayanan Sirri”), matsawar cewa an bayyana shi a matsayin na sirri ko aka muhimmantahi a ƙarshen bayyanawar ko kuma ya kamata ɓangaren Mai Karɓa ya fahimci na sirri ne ko mai muhmmanci ne saboda yanayin bayanan da aka bayyana da kuma yanayin da yake tattare da bayyanawar. Sai dai idan an bayyana ƙarara a cikin wannan, ɓangaren Mai Karɓa zai (1) riƙe cikin sirri kuma ba zai bayyana duk wani bayanan sirri ga wani daban ba kuma (2) ba zai yi amfani da bayanan sirri ba bisa wani dalili saɓanin cika wajibcinsa da kuma aiwatar da haƙƙoƙinsa a ƙarƙashin wannan Yarjejeniya. ɓangaren Mai Karɓa zai iya bayyana bayanan sirri ga ma’aikatansa da wakilai da ‘yan kwangila da sauran wakilai da suke da halattacciyar buƙata ta sani (haɗi da, ga Meta, waɗanda suka yi haɗin guiwa da ƙananan ‘yan kwangila da aka ambata a Shahe na 11.j), matsawar cewa suna ƙarƙashin wajibcin sirrantawa wanda bai gaza kare Bayanan Sirri na ɓangaren Mai bayyanawa ba kamar yadda aka tanada a Shashe na 5 kuma cewa ɓangaren Mai Karɓa shi ne zai ɗauki nauyin biyayyar wannan mutum ga sharuɗɗan da ke wannan Shashe na 5.
- Togaciya. Wajibcin Sirrantawar ɓangaren Mai Karɓa ba zai yi aiki a kan bayanan da ɓangaren Mai Karɓa zai iya adanawa ba: (a) ya kasance ya mallake shi ne bisa haƙƙi ko kuma ya riga ya sani kafin ya karɓi Bayanan Sirrin; (b) ya zama na kowa da kowa ba ta hanyar kuskuren ɓangaren Mai Karɓa; (c) ya zama ɓangaren Mai Karɓa ya mallake shi ne bisa haƙƙi daga wani daban ba tare da karya wani wajibci na sirri ba; ko kuma (d) ya zamana ma’aikatan ɓangaren Mai Karɓa ne suka samar da shi da kansu, waɗanda ba su da damar samun waɗannan bayanai. ɓangaren Mai Karɓa zai iya bayyanawa zuwa iya abin da Dokoki ko Odar Kotu suka nema, matsawar cewa (sai dai idan doka ta hana) ɓangaren Mai Karɓa ya sanar da ɓangaren Mai Bayyanawa kafin nan kuma ya ba haɗin kai ga duk wani ynƙuri na samar da sirri.
- Samar Da Mafita. Ɓangaren Mai Karɓa ya amince cewa amfani da ko bayyana Bayanana Sirri bisa karya ƙa’idar Sashe na 5 zai iya haifar da cutar da illarta kawai ba za a iya gyara ta gama ɗaya ba, don hak cewa a yayin wannan barazana ko amfani ko bayyanawa daga Ɓangaren Mai Karɓa, Ɓangaren Mai Bayarwa yana da haƙƙin ya nemi wani abu na rage raɗaɗi ƙari a kan ko ma wane gyara doka ta tanada a kai.
- Haƙƙin mallakar kaya
- Mallakin Meta. Wannan yarjejeniya ce ta samun dama da amfani da Workplace, kuma babu wani haƙin mallaka da aka ba wa Abokin Ciniki. Kamfanin Meta da mai yi masa lasisi su ke da dukkanin haƙƙin mallaka da suna da kuɗin ruwa (haɗi da dukkanin haƙƙin mallakar fasaha) a cikin da kuma zuwa ga Workplace da Jumillar Bayanai da kowane da kuma dukkanin fasahar da ta danganta ko take da alaƙa da kuma dukkanin ayyukan da aka samar ko gyara ko ingantawa da aka yi wa dukkanin abin da ya gabata da Meta ya ƙirƙira ko a madadinsa, haɗi dangane da Martaninka (da aka bayyana a ƙasa). Babu wani haƙƙi da aka ba ka sai dai kamar yadda aka bayyana a wannan Yarjejeniyar.
- Martani. Idan ka miƙa jawabi ko tambaya ko shawara ko ka yi amfani da lamari ko sauran martani da suka danganci amfaninka da Workplace ko API ɗinsa ko sauran kayayyakinmu ko ayyuka (“Martani”), za mu iya amfani da amfanar wannan Martani dangane da kowanne daga cikin Kayayyakinmu ko ayyuka ko na abokan haɗin guiwarmu kai tsaye, ba tare da wani nauyi ko biyan diyya gare ka ba.
- Bayanin Wanke Kai
META YA BAYYANA WANKE KANSA DAGA KOWANE DA DUKKANIN GARANTI DA KOWANE NAU”IN WAKILCI, A YBAYYANE KO A AIKACE KO NA DOKA< HAƊI DA KOWANE WARANTI NA KASUWANCI, DA YA DACE DA WANI DALILI KO SUNA KO NA RASHIN KARYA DOKA. BA MU BA DA GARANTIN VEWA WORKPLACE ZAI KASANCE BA TARE DA KATSEWA KO RASHIN MATSALA BA. ZA MU IYA BA WA WANI NA DABAN DAMA YA SAMAR DA AYYUKA DA MANHAJOJIN DA SUKE TALLAFAR AMFANINKA DA WORKPLACE KO KUMA ZA MU IYA BA WA WORKPLACE DAMA YA HAƊE DA SAURAN AYYUKA DA MANHAJOJI. META BA YA ƊAUKAR NAUYIN KOWANE AYYUKA KO MANGHAJOJIN DA KA ZAƁA KA YI AMFANI DA SU DANGANE DA WORKPLACE. AMFANINKA DA WAƊANNAN AYYUKA KO MANHAJOJI YA DANGANTA DA WASU SHARUƊƊAN DA DOKOKI NA DABAN KUMA KA AMINCE KA KUMA YARDA CEWA DUK WANI HAƊARIN AMFANI A KANKA YAKE. - Iyakance Ɗaukar Nauyi
- SAI DAI IƘRARIN DA AKA KEƁE (AN BAYYANA A ƘASA):
- BA WANI ƁANGARE DA ZAI ƊAUKI NAUYIN WATA ASARAR AMFANI KO ASARA KO BAYANAI BA DAIDAI BA KO KATSEWAR CINIKI KO KUƊIN TSAIKO KO DUK WANI LAHANI KO WANE IRIR A SANADIYYA (HAƊI DA ASARAR RIBA), BA TARE DA LA’AKARI DA YANAYIN AIKIN BA KO A CIKIN KWANGILA KO SHARI’A (HAƊI DA SAKACI), ƊAUKAR NAUYI NA DOLE KO KUMA YANAYIN DA IDAN AN SANAR DA YIWUWAR SAMUN WANNAN LAHANIN KAFIN AFKUWARSA; DA KUMA
- BABU WANI ƁANGARE DA NAYINSA GABA ƊAYA GA ƊAYAN ZAI ZARCE AINAHIN ADADIN DA AKA BIYA KO WANDA ABOKOIN CINIKI ZAI BIYA META A WATANNI GOMA SHA BIYU (12) A ƘARƘASHIN WANNAN YARJEJENIYA KO KUMA IDAN BABU WANI KUƊI DA AKA BIYA KO DA ZA A BIYA A WANNAN LOKACIN, TO DALA DUBU GOMA ($10,000).
- Saboda wannan Sashi na 8,”Iƙirarin Da Aka Ware” na nufin: (a) Nauyin abokin ciniki da ya taso a ƙarƙashin Sashi na 2 (Bayananka Da Nauye-nauyen da ke kanka); da kuma (b) karya nauye-nauyen da ke kan ɓangare a Sashi na 5 (Sirrantawa) amma ban da iƙirarin da suka danganci Bayananka.
- Iyakancewar da take wannan Sashi na 8 za ta ci gaba kuma ta yi aiki ko da an samu kowace iyakar gyara da aka bayyana a wannan Yarjejeniya ta gaza dalilanta, kuma ɓangaririn sun yarda cewa ba wani ɓangare da zai iyakance ko ya ware nauyin da ke kansu ga duk wani abu da ba za a iya iyakance shi ba ko ware shi ta hanyar doka. Ka amince kuma ka yarda cewa tanadinmu na Workplace yana kan hasashen cewa nauyinmu yana da iyaka kamar yadda aka tanada a cikin wannan Yarjejeniya.
- SAI DAI IƘRARIN DA AKA KEƁE (AN BAYYANA A ƘASA):
- Wa’adin Lokaci da Ƙarewa
- Sharaɗi. Wannan Yarjejeniya za ta fara aiki a ranar da ka fara shiga Workplace ɗinka ka kuma ci gaba har sai an dakatar kamar yadda aka ba da dama a cikin nan (“Sharaɗin”).
- Ƙarewa saboda Samun nutsuwa. Ba tare da zama shaida ba ga haƙƙinka ka ƙarewa a sakin layi na 2.d na Ƙarin Dokar Sarrafa Bayanai, za ka iya kawo ƙarshen wannan Yarjejeniya a kowane lokaci ba tare da wani dalili ko da dalilin, a bisa sanarwa ga Meta kwana talatin (30) kafin nan ta hannun mai gudanarwarka da zai zaɓi y agoge Workplace ɗinka a cikin kayan. Meta zai iya kawo ƙarshen wannan Yarjejeniya a kowane lokaci ba tare da wani dalili ba ko da dalilin, a bisa sanarwa gare ka kwana talatin (30) kafin nan.
- Ƙarewa da Dakatarwa na Meta. Kamfanin Meta yana da haƙƙin ya kawo ƙarshen wannan Yarjejeniya da sanarwar da ta dace gare ka ko dakatarwa ta nan take ga damarka ta shiga Workplace idan ka karya wannan Yarjejeniya ko kuma idan muka ga hakan ya zama dole don mu kare illa ga tsaro ko daidaituwa ko samuwa ko mutuncin Workplace.
- Goge Bayananka. Meta zai goge bayananka nan take bayan kowace irin ƙarasawar wannan Yarjejeniya, amma ka san cewa share abun ciki na iya dawwama a cikin kwafin ajiya na zuwa wani lokaci a yayin da ake kan gogewar. Saiti na huɗu a Sashi na 2.e, kai kaɗai kake alhakin ƙirƙirar rumbun baya na Bayananka don amfaninka.
- Fara Aikin Ƙarewa. A duk lokacin da wannan Yarjejeniya ta ƙare: (a) dole kai da mai amfaninka ku daina amfani da Workplace nan take; (b) a bisa neman Ɓangaren Mai Bayyanawa, kuma bisa tanadin 9.d, Ɓangaren Mai Karɓa zai dawo ko ya goge duk wani Bayanan Sirri na Ɓangaren MAi Bayyanawa da yake wurinsa; (c) za ka biya Meta duk wani kuɗi da ba a biya ba wanda ya taru kafin ƙarewar; (d) idan Meta ta kawo ƙarshen wannan Yarjejeniya batare da dalili bisa Sashi na 9.b, Meta zai dawo maka da kuɗin wani biya da ake yi kafin amfani (inda hakan ke aiki); sannan (e) waɗannan Sassan za su ci gaba da aiki: 1.c (ƙayyadewa), 2 (Amfani da Bayananka da kuma nauyenauyenka) (Wani bayan lasisin Meta ga Bayananka a Sashi na 2.a) 3.b (Bayyanawa ta Shari’a da Neman Wani Na Daban), 4 (Biyan kuɗi) har zuwa na 12 (Ma’anoni). SAi dai kamar yadda aka fayyace a cikin wannan Yarjejeniya, aiwatarwar kowane ɓangare na yin gyara haɗi da ƙarewa, ba ya matsayin shaida ga duk wasu gyara da za a iya samu a ƙarƙashin wannan Yarjejeniya, bisa doka ko wanin haka.
- Sauran Asusun Facebook
- Asusun Mutum Na ƙashin Kansa. Saboda kauce w akokwanto Asusun mai amfani sun bambanta daga duk wani asusun mutum na ƙashin kansa na Facebook da mai amfani zai iya ƙirƙira a ayyukan Facebook na masu amfani da kaya (“Asusun Facebook na ƙashin kai”). Asusun Facebook Na ƙashin kai ba sa cikin wannan Yarjejeniya, sai dai suna ƙarƙashin sharuɗɗan Meta na waɗancan ayyuka, kowanne tsakanin Meta da mai amfani.
- Workplace da Tallace-tallace. Ba za mu nuna wa Masu Amfanin ka talla na wani can daban a Workplace ba kuma ba za mu yi amfani da Bayananka don mu samar ko nufi yin talla ga Masu Amfanin ka ba ko mu tsara morewar Masu Amfanin ka a kan Asusun Facebook ɗinsu na ƙashin kai ba. Duk da haka, Meta za ta iya yin sanarwar ko ta bayanar da masu gudanar da tsari game da sigogi, alaƙa ko aikatawan da ya danganci Workplace.
- Na bai-ɗaya
- Sauye-sauye. Meta zai iya sauya sharuɗɗan wannan Yarjejeniya da dokokin da aka ambata a ciki ko wannan Yarjejeniya ta haɗar da su a kowane lokaci, haɗi da, ba tare da iyakancewa ga ƙarin Dokar Sarrafa Bayanai da Dokar Aika Bayanai (don yin biyayya ka dokokin tsare bayanai da suke aiki) da Dokar Tsaron Bayanai da Dokokin Amfani da aka Amince da su, ta hanyar sanar da kai ta Imel, ta aiki ko wasu hanyoyin d suka dace (“Sauyi”). Idn ka ci gaba da amfani da Workplace kwanaki shahuɗu (14) bayan sanarwarmu, to ka amince da wannan Sauyin.
- Dokar Gudanarwa. Wannan Yarjejeniya da kuma amfanin Masu amfaninka da Workplace da kuma duk wani iƙirari da zai iya tasowa tsakanin mu da kai, doka ce take gudanar da shi, kuma dole a yi shi bisa, dokokin Amurika da jihar California, kamar yadda ake aiki da su, ba tare da barin ƙa’idojin na rikicin doka ya yi tasiri ba. Duk wani iƙirari ko sanadin aiki da ya taso daga ko ya danganci wannan Yarjejeniya ko Workplace dole a fara shi a Amurika. Kotun Lardi ta Lardin Arewacin California ko kotun jaha da ke Gundumar San Mateo, da kuma kowane ɓangare a nan ya yarda da ikon waɗannan kotuna.
- Cikakkiyar Yarjejeniya. Wannan Yarjejeniya (wadda ta haɗa da Dokar Amfani da aka aminta da ita) ita ce cikakkiyar yarjejeniya tsakanin ɓangarori dangane da damarka ta shiga da amfani da Workplace kuma ta shafe duk wani wakilci ko yarjejeniya da suka danganci Workplace a baya. Kanun bayanai don jin daɗi ne kawai, sannan sharuɗɗa kamar “haɗi da” za a yi su ne ba tare da iyaka ba. An rubuta yarjejeniyar da Ingilishi (na Amurka), wanda shi ne zai kula da duka samfurin da aka fassara.
- Afuwa da Ci gaba da aiwatarwa. Kasa aiwatar da wani tanadi ba za a ɗauke shi afuwa ba; Dole afuwa ta zama a rubuce da sa hannun ɓangaren da ake iƙirarin ya yi afuwar. Duk wasu sharuɗɗa ko sharuɗɗa a kowace odar siyayya ta Abokin ciniki ko yanayin kasuwanci ba zai sauya wannan Yarjejeniya ba kuma a nan an bayyana ƙin amincewa da su, kuma duk irin wannan daftari zai kasance don gudanarwa ne kawai. Idan wata kotu da take hurumi ta yi hukuncin cewa wani daga cikin danadin wannan Yarjejeniya ba zai aiwatu ba ko ba shi inganci ko kuma ya saɓa wa doka, za a bayyana wannan tanadin ta yadda zai cika buradunsa iya iyawa kuma suaran tanade-tanaden wannan Yarjejeniya za a aiwatar da su kuma suna aiki
- Yaɗawa. Duk wata takardat manema labarai da aka saki ko neman kasuwa game da alaƙar ɓangarori yana buƙatar amincewar ɓangarorin a rubuce kafin nan. Ba tare da la’akari da abin da ya gabata ba: (a) a cikin kamfaninka za ka iya yayata ko haɓaka amfani da Workplace yayin aiki a ƙungiyance (misali kaƙarfafa guiwar karɓar masu amfani), bisa ƙa’idojin da alamar Meta da ake tanada lokaci zuwa lokaci, da kuma (b) Meta zai iya ambatar sunanka da matsayinka a matsayin mai anfani da Workplace.
- Sanya Aiki. Ba wani ɓangare da zai sanya wannan Yarjejeniya ko haƙƙoƙinta ko nauye-nauyen da ke ƙarƙashin wannan Yarjejeniya ba tare da amincewar ɗaya ɓangaren a rubuce kafin hakan ba, sai dai cewa Meta za iya sanya wannan Yarjejeniya ba tare da amincewar wani abokin haɗin guiwarta ba ko dangane da haɗaka, sake tsari, samu ko mayar da dukkanin ko kusan dukkanin kadarorinta ko ƙuri’ar tsaro. Dangane da abin da ya gabata, wannan Yarjejeniya za ta yi aiki kuma tabbatar da amfanin kowane ɓangare na ba da damar magaji ko sanyawa. Sanyawar da ba a ba da izini ba ɓatacciya ce kuma ba za ta ɗora nauyi a kan Meta ba.
- Ɗan Kwaniga Mai Zaman Kansa. Ɓangarorin ‘yan kwangila masu zaman kansu. Babu wata hukuma ko ƙawance ko haɗin gwiwa ko aiki da aka samar a sanadiyyar wannan Yarjejeniya kuma babu wani ɓangare da yake da ikon tirsasa ɗayan.
- Babu Cin Moriyar Wani Can Daban. Wannan Yarjejeniya tana amfanar Meta ne da Abokin ciniki don haka babu wani nufin cin moriya ga wani can daban, haɗi da kowanne mai amfani.
- Sanarwa. A yayin da kake ƙare wannan Yarjejeniya bisa Sashi na 9.b dole ka sanar da Meta ta hannun mai gudanar da tsarinka, da zai zaɓi goge Workplace ɗinka daga kayan. Duk wata sanarwa a ƙarƙashin wannan Yarjejeniya, dole ta zamo a rubuce a aika wa Meta ta wannan adireshi (kamar yadda yake aiki): Idan Meta Platforms Ireland Ltd ne, zuwa ga 4 Grand Canal Square, Dublin 2, Ireland, Attn: Ɓangaren Shari’a kuma idan Meta Platforms Inc ne, zuwa ga 1 Hacker Way, Menlo Park, CA 94025 USA, Attn: Ɓangaren Shari’a. Meta zai iya aika sanarwa zuwa ga adireshin imel ɗin da ke kan asusun Abokin ciniki. Haka kuma Meta zai iya samar sanarwar ayyuka da suka jiɓanci Workplace ko wasu sanarwar da suka danganci kasuwanci ta hanyar saƙo ga mai amfani a cikin Workplace ko aike na haɗin baki a cikin Workplace.
- Ƙaramin Ɗan Kwangila. Meta zai iya amfani da ƙananan ‘yan kwangila ta kuma ba su dama su aiwatar da haƙƙoƙin Meta a ƙarƙashin wannan Yarjejeniya, amma Meta zai ci gaba da ɗaukar alhakin yin biyayyar irin wannan ƙaramin ɗan kwangila ga wannan Yarjejeniya.
- Fin Ƙarfin Aiwatarwa. Babu wani ɓangare da zai ɗauki nauyin wani saboda kowane tsaiko ko kasa aiwatar da wani nauyi a ƙarƙashin wannan Yarjejeniya (sai dai kasa biyan kuɗi) idan tsaikon ko kasawar saboda wasu abubuwa da ba ahango ba da suka faru bayan sa hannu a wannan Yarjejeniya kuma sun fi ƙarfin wannan ɓangare, kamar yajin aiki ko tare hanya ko yaƙi ko aikin ta’addanci ko zanga-zanga ko annoba ko katsewa ko lalacewar lantarki ko hanyar sadarwa ko sadarwar bayanai ko ayyuka, ko hana lasisi ko izini daga hukumar gwamnati ko wani.
- Shafukan Yanar-gizo na Wasu Daban. Workplace zai iya ƙunsar kafa zuwa ga shafin yanar gizo na wani can daban. Wannan ba yana nufin mun aminta da wannan shafin yanar gizon ba kuma ba ma ɗaukar nauyin ayyuka ko bayanai ko bayani na shafin yanar gizo na wani can daban ko ayyuka ko duk wata kafa da suka ƙunsa a ciki ko wani sauyi ko sabuntawa da aka yi musu. Shafin yanar gizo na wani can daban zai iya tanadar sharuɗɗa da dokokin amfani nasa da dokokin sirri da suke aiki a kanka da Masu amfaninka da kuma wannan Yarjejeniya ba ta kula da amfaninka da irin wannan shafin yanar gizon na wani can daban.
- Kula Da Fitar Da Kaya Da Takunkumin Kasuwanci. A amfani da Workplace abokin ciniki ya yarda ya yi biyayya ga dukkanin dokoki da ƙa’idojin shigowa da fitar da kaya na Amurka da kuma sauran dokokin da suke aiki, da kuma duk wani takunkumi ko taƙaitawar kasuwanci. Ba tare da taƙaita abin da ya gabata ba abokon ciniki yana wakilta kuma ya ba da waranti cewa: (a) ba a jera shi a cikin jerin ɓangarorin da aka haramta ko taƙaita na Amurika ba; (b) bai shiga cikin wani takunkumin tattalin arziƙi ko taƙait akasuwanci na Majalisar Ɗinkin Duniya ko Amurika ko Tarayyar Turai ko wani da ake aiki da shi ba; kuma (c) ba ya aiki ko masu amfani a ƙasashen da takunkumin kasuwancin Amurika ya shafa ba.
- Ƙa’idojin Amfanin Hukumar Gwamnati. Idan kai Hukumar Gwamnati ne, kana wakiltar cewa: (i) babu wata doka ko ƙa’ida da suka hana ka yarda da aiwatarwa ko yarda da aiwatarwa na wani sharaɗi ko ƙa’idar wannan Yarjejeniya, (ii) babu wata doka ko ƙa’ida da za su sa ba za a iya aiwatar da wani shaɗi ko ƙa’idar wannann Yarjejeniya ba a kanka ko wata Hukuma ta Gwamnati, (iii) kana da izini kuma kana da iko a shari’ance bisa dokoki da ƙa’idojin da ake da su ka wakilta ka kuma ɗora wa kowace Hukumar Gwamnati wannan Yarjejeniya; sannan (iv) ka shiga wannan Yarjejeniya ne ba bisa shawarar san zuciya ba, sai ta la’akari da ƙimar Workplace gare ka da Masu amfaninka kuma ba wani son zuciya ko biyan buƙata da suka sa ka yanke shawarar shiga wannan Yarjejeniya. Kada ka shiga cikin wannan Yarjejeniya idan ba za ka iya yin wakilcin da ke cikin wannan Sashi na 11.n ba. Idan Hukumar Gwamnati ta shiga wannan Yarjejeniya bisa saɓa wa wannan Sashi na 11.n, Meta zai iya zaɓar kawo ƙarshen wannan Yarjejeniya.
- Masu Sake Sayarwa. Za ka iya zaɓar ka shiga ka kuma yi amfani da Workplace ta hanyar Mai sake sayarwa A yanayin da ka shiga ka kuma yi amfani da Workplace ta hannun Mai sake sayarwa, kai kaɗai kake da alhakin: (i) duk wani haƙƙi na dangantaka da nauye-nauye a yarjejeniyarka da Mai sake sayarwa, kuma (ii) a tsakaninka da Meta duk wata shigar Mai sake sayarwa cikin Workplace ɗinka da Bayananka da duk wani asusun mai amfani da za ka iya ƙirƙira don Mai sake sayarwarka. Bugu da ƙari, a yanayin da ka shiga ka kuma yi amfani da Workplace ta hannun Mai sake sayarwa, to ka amince cewa Sharuɗɗan Abokin ciniki Mai sake sayarwa su za su yi aiki a kan duk wasu sharuɗɗa masu rikici a cikin wannan Yarjejeniya.
- Ma’anoni
a wannan Yarjejeniya, sai dai idan an faɗi saɓanin haka:“Dokar Amfani Da Aka Aminta da ita” na nufin dokokin amfani da Workplace , wanda za a samu a www.workplace.com/legal/FB_Work_AUP, kamar yadda za a iya gyara su lokaci zuwa lokaco. “Haɗin Guiwa” na nufin wanda ya mallaka ko yake kula ko aka mallake shi ko ake kula da shi ko yake ƙarƙashin mallaka ko kula ta bai ɗaya da wani ɓangare, inda “kula” take nufin ikon ba da umarnin gudanarwa ko harkokin abu, kuma “mallaka” take nufin mallki mai amfani na kaso 50% (ko, idan iyaka ba ta bayar da damar mallakar mafi yawa ba, to mafi yawan adadin abin da dokar ta ba da dama) ko kuma yawan ƙuri’ar hannun jari ko wani daidaiton adadin ƙuri’a. Saboda wannan ma’ana, Hukumar Gwamnati ba abokiyar haɗin guiwar wata Hukumar Gwamnati ba ce sai dai idan tana da cikakken ikon kula da wannan Hukumar Gwamnatin. “Ƙarin Dokar Sarrafa Bayanai” na nufin ƙarin dokar sarrafa bayanai da aka maƙala wa kuma ya zama wani ɓangare na wannan Yarjejeniya, haɗi da duk wasu sharuɗɗan da aka ambata a ciki. “Ratayen Tsaron Bayanai” na nufin ratayen tsaron bayanai da aka maƙala wa kuma ya zama wani ɓangare na wannan Yarjejeniya. “Hukumar Gwamnati” na nufin duk wata ƙasa ko yanki mai iko a Duniya, haɗi da ba tare da iyakancewa ba, duk wata jiha ko ƙaramar hakuma ko gunduma ko yanki ko wani rukuni ko rabo na siyasa na gwamnati ko duk wata ma’aikatar gwamnati ko Kasuwanci ko wani abu da wannan gwamnati ta kafa ko ta mallaka ko take kula da kuma duk wani wakilci ko wakili na kowanne daga cikin abubuwan da suka gabata. “Dokoki” na nufin dukkanin dokoki da ƙa’idoji da yarjejeniya na gida da na jiha da na tarayya da na ƙasa da ƙasa, haɗi da ba tare da iyakancewa ba, waɗanda suka danganci sirrin bayanai da aika bayanai da sadarwar ƙasa da ƙasa da fitar da bayanan fasaha da na mutum da samar da kayan jama’a. "Mai sake sayarwa" yana nufin wani abokin hulɗa na daban wanda ke da ingantacciyar yarjejeniya da Meta da ke ba su izinin sake sayarwa da samar da damar shiga Workplace. “Sharuɗɗan Abokin Ciniki Mai sake Sayarwa”yana nufin sharuɗɗan da ake samu a https://www.workplace.com/legal/FB_Work_ResellerCustomerTerms, kamar yadda za a iya sabuntawa daga lokaci zuwa lokaci, da kuma yake ɓangaren wannan Yarjejeniya, kuma ya kasancewa ƙarin sharuɗɗa tsakanin ɓangarorin da suka shafe ka, idan ka shiga kuma ka ui amfani da Workplace ta hanyar Mai sake sayarwa. "Masu amfani" yana nufin kowane daga ko ma’aikatan Kamfanonin da ke ƙarƙashinka, ‘yan kwangila ko wasu ɗaiɗaikun mutane da ka ba damar shiga Workplace. "Workplace" yana nufin aikin Workplace da mu ke samarwa gareka ƙarƙashin wannan Yarjejeniya, da kuma duk wani samfurin da zai zo, da ya haɗa da duk wasu shafukan yanar-gizo, manhajoji, ayyukan kan intanet, kayan aiki, da kuma bayanan da za mu iya samar maka ƙarƙashin wannan Yarjejeniya, kamar yadda za a iya gyarawa daga lokaci zuwa lokaci. “Bayananka” na nufin (a) duk wani bayanin tuntuɓa ko na hanyar sadarwa ko bayanan rijistar asusu da kai ko Mai amfaninka kuka miƙa zuwa ga Workplace; (b) duk wani bayani ko bayanai da kai ko Masu amfaninka kuka wallafa ko aika ko raba ko kuka shigo da shi ko kuka samar a kan Workplace; (c) bayanan da muka tattara yayin da kai ko Masu Amfaninka kuka tuntuɓe mu ko kuka neme mu don tallafin da ya danganci Workplace, haɗi da bayanai game da na’ura da manhaja da sauran bayanai da aka tattara da suka danganci ba da tallafi; da kuma (d) Duk wani bayanin amfani ko na aiki (misali Adreshin IP da burauza da nau’in tsarin aiki da shaidar na’ura) da ya danganci yadda Masu amfani suke mu’amala da Workplace. “Dokokinka” na nufin dokokinka da suke aiki na ma’aikata ko tsari ko sirri ko HR ko ƙorafi ko wasu dokoki.
Ratayen Sarrafa Bayanai
- Ma’ana
A cikin wannan Ratayen Sarrafa Bayanai, “GDPR” na nufin Tsarin Kare Bayani Na Bai Ɗaya (Doka (EU) 2016/679), da “Jagora”, “Masarrafin Bayanai”, “Batun Bayanai”, “Bayanai na Ƙashin Kai”, “Saɓa Bayanai na ƙashin kai” da “Sarrafawa” za su kasance suna da ma'ana iri ɗaya kamar yadda aka ayyana a cikin GDPR. “Sarrafaffe” da “Sarrafawa”za a fassara daidai da ma'anar "Sarrafawa”. A daidai da tanadin GDPR da tanade-tanadensa a ciki har da GDPR kamar yadda aka yi wa dokara gyara aka saka ta a dokar Burtaniya. Duk sauran ƙayyadaddun sharuɗɗan da ke cikin wannan za su sami ma'ana iri ɗaya kamar yadda aka ayyana a wani wuri a cikin wannan Yarjejeniyar. - Sarrafa Bayanai
- A yayin gudanar da ayyukan a matsayin Mai sarrafawa a ƙarƙashin wannan Yarjejeniyar dangane da kowane Keɓaɓɓen Bayanan da ke cikin Bayanan ku (“Bayanai na Ƙashin kai”), Meta ya tabbatar da cewa:
- tsawon lokaci, batun da ake magana, yanayi da manufar Sarrafawar za su kasance kamar yadda aka ƙayyade a cikin Yarjejeniyar;
- nau'ukan Bayanan da aka Sarrafa za su haɗa da waɗanda aka ƙayyade a cikin ma'anar Bayanan ku;
- Rukunin Batutuwan Bayanai sun haɗa da wakilanku, Masu amfani da duk wasu mutane da aka gano ko gano su ta Bayananku na Ƙashin kai; kuma
- wajibcinku da haƙƙoƙinku a zaman Mai Kula da Bayanai dangane da Bayananku na Ƙashin kai an tsara su a cikin wannan Yarjejeniyar.
- Har ya kai Meta yana sarrafa Bayananku na Ƙashin kai ko dangane da Yarjejeniyar, Meta zai:
- kawai Sarrafa Bayananku na Ƙashin kai daidai da umarnin ku kamar yadda aka tsara a ƙarƙashin wannan Yarjejeniyar, gami da batun canja wurin Bayananku na Ƙashin kai, dangane da kowane abun da aka kange wanda doka ta 28 (3) (a) na GDPR ta aminta;
- tabbatar da cewa waɗancan ma'aikatanta da aka ba su izinin Sarrafa Bayananku na Ƙashin kai A ƙarƙashin wannan Yarjejeniya sun miƙa wuya ga sirrantawa ko kuma suna ƙarƙashin wajibcin sirrin da ya dace na sirrantawa dangane da Bayananku na Ƙashin kai;
- aiwatar da matakan fasaha da ƙungiyoyi da aka tsara a cikin Ratayen Tsaro na Bayanai;
- mutunta sharuɗɗan da aka ambata a ƙasa a cikin Sashe na 2.c da 2.d na wannan Ratayen Sarrafa Bayanai lokacin naɗa ƙananan Masu sarrafawa;
- taimaka muku ta matakan fasaha da ƙungiyoyi masu dacewa, gwargwadon yadda hakan zai yiwu ta Wurin Aiki, don ba ku damar cika haƙƙoƙin ku don amsa buƙatu don aiwatar da Haƙƙoƙin Sirrin ta hanyar Ayyuka a ƙarkashin Babi na III na GDPR;;
- taimaka muku wajen tabbatar da biyan bukatunku bisa ga Dokoki na 32 zuwa 36 GDPR la'akari da yanayin Sarrafawa da bayanan da ke akwai ga Meta;
- a kan ƙarewar Yarjejeniyar, share Bayanan Ƙashin kai bisa ga Yarjejeniyar, sai dai idan Tarayyar Turai ko Dokar Ƙasa ta buƙaci a riƙe Bayananku na Ƙashin kai;
- samar da bayanan da aka bayyana a cikin wannan Yarjejeniyar kuma ta Wurin Aiki a cikin gamsuwa da wajibcin Meta don samar da duk bayanan da suka wajaba don nuna yarda da wajibcin Meta a ƙarƙashin Doka ta 28 ta GDPR; kuma
- bisa ga shekara-shekara, sayan zai kasance ta mai bincike na waje da zaɓin Meta ya gudanar da SOC 2 Nau'in II ko wasu ma'aunai na masana'antu na sarrafa Meta da ke da alaƙa da Wurin Aiki, irin wannan mai binciken na ɓangare na waje wanda kuke ba da izini. A buƙatar ku, Meta zai samar muku da kwafin rahoton binciken sa na yanzu kuma irin wannan rahoton za a ɗauki bayanin Sirri na Meta.
- Kuna ba da izini Meta don ƙaddamar da wajibcin Sarrafa bayanansa a ƙarƙashin wannan Yarjejeniyar zuwa Ƙungiyoyin Meta, da kuma ga wasu ɓangarori na waje, jerin wanda Meta zai ba ku a kan buƙatun ku a rubuce. Meta za ta yi haka ne kawai ta hanyar yarjejeniyar da aka rubuta tare da irin wannan mai Sarrafawa wanda ke ɗora nauyin kariya iri ɗaya a kan mai Sarrafawa kamar yadda aka sanya a kan Meta a ƙarƙashin wannan Yarjejeniyar. A yayin da wannan ƙaramin mai Sarrafawa ya gaza sauke wannan nauyi, Meta ne zai ɗauki alhakin ƙwazon sauke nauyin wannan ƙaramin mai sarrafawa.
- Inda Meta ya shigar da ƙarin ko maye gurbin ƙaramin mai ko masu Sarrafawa, Meta zai sanar da kai wannan ƙarin ko maye gurbi ƙananan masu Sarrafawa cikin kwanakin da ba su wuce goma sha huɗu (14) ba kafin naɗin wannan ƙarin ko maye gurbin ƙananan masu Sarrafawa Kuna iya ƙin haɗa irin wannan ƙarin ko sauyawa ƙananan masu Sarrafawa a cikin kwanaki goma sha huɗu (14) bayan Meta ya sanar da ku ta hanyar ƙare Yarjejeniyar nan da nan a kan rubutacciyar sanarwa ga Meta.
- Meta zai sanar da kai ba tare da ɓata lokaci ba a kan sanin Keta Bayanan Sirri da ke da alaƙa da Bayananku na Ƙashin kai. Irin wannan sanarwar za ta haɗa da, a lokacin sanarwa ko kuma da wuri-wuri bayan sanarwar, cikakkun bayanai masu dacewa na Keta Bayanan Sirri idan ya yiwu, gami da adadin bayanan da abin ya shafa, nau'i da kimanin adadin Masu amfani da abin ya shafa, sakamakon da ake tsammani na cin zarafi. da duk wani ainihin ko shawarwarin magunguna, inda ya dace, don rage yiwuwar illar ɓarnar.
- Har zuwa GDPR ko dokokin kariyar bayanai a cikin EEA, UK ko Switzerland sun shafi Sarrafa da Bayananku a ƙarƙashin wannan Rataye sarrafa BayanaiRatayen Musayar Bayanai na Turai ya dace da canja wurin bayanai ta Meta Platforms Ireland Ltd kuma ya samar da wani yanki na, kuma an haɗa shi ta hanyar tunani a cikin, wannan Ratayen Sarrrafawa Bayanai.
- A yayin gudanar da ayyukan a matsayin Mai sarrafawa a ƙarƙashin wannan Yarjejeniyar dangane da kowane Keɓaɓɓen Bayanan da ke cikin Bayanan ku (“Bayanai na Ƙashin kai”), Meta ya tabbatar da cewa:
- Sharuɗɗan Sarrafawa na Amurka
- Har zuwa lokacin da Sharuɗɗan Sarrafawa Meta ta Amurka suka yi amfani da su za su zama wani ɓangare na, kuma an haɗa su ta hanyar tunani a cikin wannan Yarjejeniyar, adana don Sashe na 3 (Wajibi na Kamfanin) wanda aka keɓe.
Sharuɗɗan Tsaron Bayanai
- Share Fage da Dalili
wannan daftari ya bayyana mafi ƙanƙantar tsaron da ake buƙata da ake aiki da shi wajen samar da Workplace da Meta ta yi gare. - Tsarin Kula Da Tsaron Bayanai
Meta ya samar kuma zai tabbatar da Tsarin Kula Da Tsaron Bayanai (ISMS) da aka tsara shi don ya aiwatar da ingantattun ayyukan tsaron bayanai na kamfani, waɗanda take aiki da su wajen samar da Workplace. An tsara Tsarin Meta na ISMS don ya kare shiga ko bayyanawa ko amfani ko gyara bayananka ba tare da izini ba. - Tsarin Kula Da Haɗari
kayayyakin tsaron bayanai da na sarrafa bayanai, haɗi da Kayayyakin IT da kayayyki na zahiri, za su kasance bisa tsarin kula da haɗari. Za a riƙa gudanar da auna haɗarin Workplace a kai a kai. - Tsara Tsaron Bayanai
Meta yana da jami’in tsaro da aka ɗorawa alhakin dukkanin tsaro a ma’aikatar. Meta yana da jami’an tsaro da aka ɗora wa alhakin sa ido a kan tsaron Workplace ɗinka. - Tsaron na Zahiri da na Muhalli
Matakan tsaron Meta sun haɗa da tsara kula da za ta samar da tabbaci daidai gwargwado na taƙaita damar shiga cikin gine-ginen sarrafa bayanai na zahiri ga waɗanda aka ba izini da kuma cewa an samar da kula ta muhalli don a gano, kare a kuma kula da lalacewar kaya saboda haɗuran muhalli. Kular ta haɗa da: Kular ta haɗa da:- Shiga da kuma bincika shigar ma’aikata da ‘yankwangila ta zahiri cikin gine-ginen sarrafa bayanai;
- Samar da kyamarar tsaro a muhimman wuraren shiga gine-ginen sarrafa bayanai;
- Tsarin da yake lura da sarrafa yanayin zafi da danshi saboda kayayyakin kwamfuta; da kuma
- Samar da wutar lantarki da janareton ko ta kwana.
- Warewa
Meta zai samar da matakai na fasaha da aka tsara su don su tabbatar cewa an ware Bayananka cikin hikima daga bayanan saura abokin ciniki kuma cewa masu amfanin da aka ba wa izini ne kaɗai suke samun Bayananka. - Ma’aikatan Meta
- Ba Da Horo
Meta zai tabbatar cewa dukkanin ma’aikatan da suke da damar samun Bayananka sun sami horo a kan tsaro. - Tantancewa da kuma Binciken Halayya
Meta zai:- Sami wani tsari na tantance shaidar ma’aikatan da suke aiki tare da Workplace ɗinka.
- Sami wani tsari na gudanar da bincike halayya a kan ma’aikatan da suke aiki tare da Workplace ɗinka bisa tsayayyen tsarin Meta.
- Karya Tsaron Ma’aikata
Meta zai samar da takunkumi damar samun Bayananka mara izini ko wadda ba a yarda ba ga ma’aikata Meta, haɗi da hukunci har zuwa kuma ya haɗar da kora.
- Ba Da Horo
- Gwajin Tsaro
Meta zai riƙa gudanar da gwajin tsaro da na haɗari a kai-a kai don ya auna ko ana aiwatar da muhimmiyar kulawa yadda ya kamata kuma tana aiki. - Kula da Samun Dama
- Kula Da Lambar Sirrin Mai Amfani
Meta zai samar da tsare-tsaren kula da lambar sirrin Mai Amfani, da aka tsara don a tabbatar kowanne mutum yana da lambar sirrinsa, kuma wanda ba shi da izini ba zai iya samun ta ba, haɗi da mafi ƙanƙanta:- Samar da lambar sirri, haɗi da tantance shaidar mai amfani kafin sabuwa ko sauyawa lambar sirri ko ba da ta wucin gadi.
- Sanya dukkanin lambar sirri cikin zaurance idan an adana su a kwamfuta ko a yayin aika su, ta hanyar sadarwa.
- Sauya dukkanin lambobin sirri na asali daga dillalai;
- Lambar sirri mai ƙarfi dangane da amfanin da za a yi da ita.
- Wayar da kan mai amfani
- Kula da Damar Shigar Mai Amfani
Meta zai aiwatar da tsari na sauyawa ko ƙwace haƙƙin damar shiga da Shaidar mai amfani, ba tare da ɓata lokaci ba. Meta zai samar da tsare-tsare don kai rahoto da ƙwace damar bayanan da aka raunata (lambar sirri, tokin da sauransu); 24/7. Meta zai aiwatar da tsaron shiga da suka dace haɗi shaidar mai amfani dalokacin aukuwar sha'ani. Za a daidaita agogo da NTP Waɗannan mafi ƙanƙantar sha'ani za su zama na shige su- Izini Yana Sauyawa;
- Tantancewar da ta yi nasara da wadda ba ta yi ba da kuma yunƙurin samun damar shiga; da kuma
- Ayyukan karanta ka rubuta
- Kula Da Lambar Sirrin Mai Amfani
- Tsaron Sadarwa
- Tsaron Hanyar Sadarwa
Kamfanin Meta zai samar da fasahar da ta dace da darajar kamfani don rarrabe hanyar sadarwa. Shiga hanyar sadarwa daga nesa zuwa tsarin Meta zai buƙaci sadarwa cikin zaurance ta hanya amfani da tsarin tsaro da kuma amfani da tantancewa mai matakai. - Kare Bayani A Yayin Aikawa
Kamfanin Meta zai ɗabbaƙa amfani da tsare-tsaren da suka dace waɗanda aka shirya su don kare sirri bayanai a hanyar sadarwar jama’a.
- Tsaron Hanyar Sadarwa
- Tsaron Gudanarwa
Kamfanin Meta zai samar kuma zai tabbatar da shirin kula da haɗari ga Workplace, wanda ya haɗar da fayyace ayyuka da nauye-nauyen da ke kan kowa mallaka ta sadaukarwa don kula da haɗari, da auna yiwuwar haɗari da kuma tura faci. - Kula da Lamarin Tsari
Kamfanin Meta zai samar ya kuma tabbatar da tsarin kai ɗauki ga lamarin tsaro don kula da ganowa da warware lamuran tsaro da suka shafi Workplace ɗinka. Shirin kai ɗauki ga lamarin tsaro a ƙalla ya ƙunshi bayyana ayyuka da nauyin da ke kan kowa, da sadarwa da sake duba musabbin faruwar abu, haɗi da tantance ainahin musabbabi da shirin gyara. Kamfanin Meta zai kula da duk wani karyewar tsaro da ayyukan zargi da suka shafi Workplace. Tsarin sa ido da dabarun ganowa za a tsara su don su ba da damar gano lamarin tsaro da yake shafar Workplace ɗinka bisa barazanar da ta dace da kuma tattara bayanai game da baraza. - Ci Gaba Da Kasuwanci
Meta zai tabbatar da shirin ci gaba da kasuwanci don kai ɗauki ga yanayin gaggawa ko sauran matsanantan yanayin da za su iya yi illa ga Workplace ɗinka. Meta zai sake duba shirin ci gaba da kasuwancinsa a hukumance, a ƙalla sau ɗaya a shekara.
Sabuntawar ƙarshe: 27 ga watan Maris 2023